Ɗan takarar shugaban kasa a na jam’iyyar LP, a zaɓen da ya gabata, Peter Obi, ya bayyana zaɓen shugaban Kasa da aka yi a Najeriya a watan Faburairu a matsayin zaɓen da yafi kowacce zaɓe da aka taɓa yi a tarihin Najeriya muni.
Peter Obi ne ya zo na uku a zaɓen shugaban kasa da aka yi a Najeriya a watan Faburairu.
Ɗan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu ne yayi nasara a zaɓen inda ya kada Atiku Abubakar na PDP da shi Peter Obin na jam’iyyar LP.
A tattaunawa da yayi da Talabijin ɗin Channels, ranar Alhamis, Obi ya ce zaɓen shugaban kasan da aka yi ya yi munin da ba shi misaltawa kai tsaye.
” Ko kuri’un da aka ce na samu a Legas, an yi min Ƙwange ne, gaskiyar magana ita ce ya zaftare min kuri’u ne amma sun fi haka.
Da aka tambaye shi ko me ya sa ya ce zaɓen ita ce mafi muni tarihin kasar nan, Obi ya ce rashin amfani da bayanan BVAS yadda ya kamata na daga cikin abin da ya lalata ingancin zaben.
Tun bayan zaɓen da aka yi a watan Faburairu, Obi ya ke cewa bai yarda da sakamakon zaɓen ba.
Bayan haka ya lashi takobin sai ya kwato nasarar daga hannun Tinubu na APC a kotu.
Obi dai shine ya zo na uku a zaɓen shugaban kasan, amma duk da haka ya ce shine ya yi nasara a zaɓen, cewa ƴan Najeriya sun zaɓe ni fiye da sauran ƴan takarar, ba dun mrɗiya da aka yi min ba.