Jam’iyyar APC ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Bauchi, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta bayyana cewa PDP ce ta yi nasara.
APC ta yi zargin cewa an ɗibga maguɗi a zaɓen, kamar yadda Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Felix Morka ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.
APC ta nemi INEC ta bayyana irin aringizon ƙuri’un da ita APC ɗin ke zargin an yi.
Haka kuma jam’iyyar ta yi zargin an yi walle-walle da na’urorin tantance masu rajistar zaɓe, wato BVAS, kuma an yi hargitsi a wurare da dama.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin rundunar Bala ta tarwatsa gangamin APC a ‘gumurzun Dajin Yankari’.
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya yi nasarar zarcewa kan kujerar sa a zango na biyu, inda ya yi nasara da ƙuri’u 525,280, kamar yadda INEC ta bayyana.
Baturen Zaɓe Farfesa Abdulkarim Abubakar na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya ce Bala na PDP ya yi nasara kan Sadique Abubakar na APC, wanda ya samu ƙuri’u 432,272.
Ya ce an Halilu Jika na NNPP ya samu ƙuri’a 60,496.
Bala ya yi nasara a ƙananan hukumomi 15 daga cikin 20, waɗanda su ka haɗa da Toro, Tafawa Ɓalewa, Ningi, Alƙaleri, Dass, Ganjuwa, Zaki, Shira, Dambam Itas/Gadau, Warji, Ɓogoro, Jama’are da Kirfi.
Shi kuma Abubakar na APC ya samu Katagum, Misau, Darazo, Gamawa da Giaɗe.