Magoya bayan jami’yyar PDP sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna inda suka kalubalanci bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamna da aka yi.
Kungiyar wanda ya kunshi mata da matasa ‘yan jami’yyar PDP sun yi tattaki a manyan titunan Kaduna inda suke kira da amika wa Isah Ashiru nasarar da aka baiwa Uba Sani.
Idan ba a manta ba Uba Sani na jami’yyar APC ne hukumar zabe INEC ta bayyana ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna.
Bisa ga alkaluman zaben da INEC ta fitar ya nuna Uba Sani ya yi nasara akan Ashiru da kuri’u 10,000.
Shugaban kungiyar Aishatu Madina ta ce zaben na cike da rashin gaskiya da magudi.
Aishatu ta ce magudi da karfa-karfa aka yi a wannan zabe kuma ba za su daina yin kira ga haka ba har sai an baiwa wanda ya yi nasara a zaben wato Isah Ashiru.
“ Muna da kananan hukumomi 23 a jihar Kaduna a cikinsu jami’yyar PDP ta yi nasara a kujerun majalisar dokoki 20, majalisar dattawa duk 3 da majalisar wakilai 10 cikin 16 amma kuma wai ace sun kasa yin nasara a zaben gwamna, kun san akwai abin tambaya a ciki.
Aishatu ta ce Isah Ashiru na jami’yyar PDP ne ya yi nasara a zaben.
Haka kuma a tattaunawa da dan takarar yayi da wasu magoya bayan jam’iyyar, Ashiru ya ce tabbas murde musu zaben aka yi kuma suna nan suna tattara makaman yakin su domin kalubalantar zaben a Kotu.