Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.
Farfesa Armaya’u Hamisu, jami’in zabe na INEC ne ya bayyana hakan bayan kammala tattara sakamakon zaben daga kananan hukumomi 23 na jihar, ranar Lahadi a Sokoto.
Hamisu, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar tarayya Dutsin-ma, ya ce Aliyu ne ya lashe zaben da kuri’u 453,661.
Ya ce Malam Sa’idu Umar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u 404,632.
Jami’in zaben ya ce jam’iyyu 17 ne suka halarci zaben.
Ya kara da cewa daga cikin masu kada kuri’a 2,172,056 a jihar, mutane 901,513 ne aka tantance suka kaɗa zaben.
“Kuri’un da jam’iyyunsuka samu sune: AA kuri’u 66; AAC 207 kuri’u; ADC 329 kuri’u; ADP 1,429 kuri’u; APC ta samu kuri’u 453,661; APGA 861 da APM 232.
“Sauran su ne APP 155 kuri’u;, BP 101 kuri’u;, LP kuri’u 251; NNPP 427 kuri’u; NRM 927 kuri’u;, PDP 404,632; PRP 522 kuri’u; SDP 286 kuri’u; YPP 212 kuri’u da ZLP 113.”
Discussion about this post