Jam’iyyar ADC ta yi kira da PDP da LP su haƙura kawai, su daina jayayya da sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana Bola Tinubu na APC ya yi nasara.
Jam”iyyun biyu dai sun zargi INEC da tafka masu rashin adalci har ejan-ejan na su su ka fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Har ta kai su Atiku da Obi su ka yi kiran a dakatar da bayyana sakamakon zaɓe, kuma Shugaba INEC shi ma su ka ce ya sauka.
Amma ADC ta bakin Shugabar Kwamitin Dattawa, Patricia Akwashiki, ta ce ba su da wata jayayya, kuma ba su tare da PDP da LP.
Sannan kuma ta yi kira cewa a cire sunan ADC daga cikin jam”iyyun da aka ce su na jayayya, domin ba a yi shawara kafin a saka sunan ADC ba.
PDP da LP sun nemi Shugaban INEC ya sauka, Hukumar Zaɓe ta ce masu ‘kun yi kaɗan’
Jam’iyyar PDP da LP sun yi kiran gaggawa cewa Shugaban Hukumar Zaɓe, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙamin sa.
Su biyun sun yi wannan kiran ne a wani taron haɗin gwiwa na manema labarai da mataimakan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyun su ka gabatar a Abuja.
Mataimakan su ne Datti Ahmed na LP da Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, a Abuja.
A taron wanda su ka kira ranar Talata, sun kuma yi kiran a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta bayyana.
Sai dai kuma tuni INEC ta maida masu martanin cewa Yakubu ba zai sauka ba, tare da cewa duk mai wani ƙorafi ya garzaya ya bi tsarin da dokar zaɓe ta ce ya kai ƙorafin sa.
Kakakin INEC Rotimi Oyekanmi ya ce akwai hanyoyin da doka ta tsara su kai ƙorafin su, amma batun su ce wai shugaban zaɓe ya sauka, to tatsuniya ko mafarki ne kawai su ke yi.
Discussion about this post