Hukumar Zaɓe ta bayyana zaɓen gwamnan Jihar Adamawa cewa bai kammalu ba, don haka za a yi ‘inkwankilusib’.
Duk da cewa sakamakon ƙarshe ya nuna cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya fi Binani yawan ƙuri’u, za a bayyana ranar da za a yi ‘inkwankilusib’ a rumfunan da zaɓen gwamna ya gagara yiwuwa a jihar Adanawa.
A ƙidayar INEC, Fintiri ya zarce Binani da ƙuri’u fiye da 30,000.
Gwamna Fintiri na da 421,524, Binani ta na da 390,275.
Fintiri ya ci ƙananan hukumomi 13 a cikin 21, ita kuma Binani ta samu takwas.
Discussion about this post