Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana dalilin da ya sa ya ce ba ya so a riƙa kiran sa “His Excellency” idan aka rantsar da shi ya kama mulkin Katsina a ranar 29 Ga Mayu.
Ya ce zai fi so a riƙa kiran sa da “Mr Governor ko kuma Malam Dikko Raɗɗa” amma ba ya so a riƙa kiran sa da “His Excellency”, har sai bayan ya kammala wa’adin sa tukunna.
Raɗɗa ya bayyana haka a ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
An zaɓi Raɗɗa a ƙarƙashin APC, ya samu ƙuri’u 859,892, ya doke Yakubu Lado na PDP, wanda ya samu ƙuri’u 486,620.
“Ni dai ba na so idan an rantsar da ni a riƙa kira na “His Excellency”, saboda kalma ce mai nuna gwamna ya cika komai, ya yi dukkan abin da ya wajaba da wanda ya kamata ya yi, da kuma nauyin da ya wajaba ya sauke.
“Amma idan za a iya kira na da His Excellency ɗin bayan na kammala wa’adi na, idan har jama’a sun ga na yi masu ayyuka masu kyau. Don haka ma har gara a riƙa kira na Mr Gobernor ya fi min sauƙi.
“Ni ina so na ji ni ina daidai da kowa, saboda ba na son ana ƙaƙaba min ‘Excellency’ ɗin nan har ana kumbura min kai. Ni zan ma fi so kawai a riƙa kira na Malam Dikko Raɗɗa.”
Idan an tuna, a 2019 ma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya cire “His Excellency” a sunan sa. Haka shi ma tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2018, an riƙa kiran sa da “Ogbeni”, maimakon “His Excellency”.
Shi kuwa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ana masa laƙabi da “Arakunrin”, wato Mister kenan da kalmar Yarabanci.
Da ya ke magana kan ajandar gwamnatin sa, Raɗɗa ya ce idan aka rantsar da shi, zai fi maida hankali ne kan matsalar tsaro wadda ta addabi Jihar Katsina.