Nasarar da Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya yi a Zamfara a ƙarƙashin PDP, ta bai wa masu nazarin siyasa mamaki. Domin za a iya kiran Dauda a matsayin ɗan marayan ɗan siyasa wanda ba shi da ƙarfi, idan aka kwatanta ƙarfin gwamnan da ya kayar, Bello Matawalle na Zamfara.
Dauda Lawal tsohon ma’aikacin Bankin First Bank ne. Sai da ya kai muƙamin Babban Darakta, sannan ya yi ritaya ya shiga siyasa.
Ya fito takara a ƙarƙashin PDP, jam’iyyar da Bello Matawalle ya zama gwamna a cikin ta, a 2019. Matawalle ya yi wa PDP butulci, inda ya fice shi da jama’ar sa, su ka koma PDP.
Babban abin takaici dangane da Matawalle, shi ne yadda ya riƙa bin ‘yan PDP ya na takura masu, bayan a fice daga jam’iyyar da ta kai shi kan kujerar gwamna.
Sai da ta kai Matawalle ya ƙulla tuggun da ya sa Majalisar Dokokin Zamfara ta tsige mataimakin sa, saboda ya ƙi ficewa daga PDP zuwa APC.
Babu wanda ya yi tsammanin Dauda zai iya kayar da Matawalle, idan aka yi la’akari da irin ƙarfin da Matawalle ke da shi a Zamfara, sannan kuma sauran tsoffin gwamnonin jihar irin su Ahmed Sani Yarima, Mamuda Shinkafi da Abdul’aziz Yari duk a cikin APC su ke.
Sai dai kuma taron dangin na su ya sha rugugin wuta daga Dauda Lawal, duk da cewa ko kansila bai taɓa yi ba.
Ba tsoffin gwamnoni kaɗai ne su ka taya Gwamna Matawalle kokawa da Dauda Lawal ba. Har da tsoffin mataimakan gwamna da aka taɓa yi a jihar, irin su Muktar Anka, Ibrahim Wakkala da wanda ke kai a yanzu, wato Hassan Nasiha.
Baya ga su akwai gungun tsoffin Kakaki-kakakin Majalisar Zamfara, irin su Bature Umar Sambo, Mamman Bawa, Sanusi Rikiji da kuma Kakakin da ke kan kujera a yanzu, Honorabul Magarya. Su sun buga da Dauda Lawal, amma ya tarwatsa gangamin da su ka yi masa. Shi Kakakin ma bai koma kan kujerar sa ba, ɗan PDP ne ya kayar da shi.
PDP ta yi nasara a Zamfara a daidai lokacin da ba ta da wani ƙarfin a zo a gani a jihar. Ba ta da kansila, ba ta ciyaman, babu kwamishina, babu minista, babu sanata mai ci, sai fa ‘Yan Majalisar Tarayya su uku kacal da su ka ƙi sauya sheƙa tare da Gwamna Matawalle. Su na ne masu wakiltar Gumi/Bukkuyum, Gusau/Tsafe da kuma Shinkafi/Zurmi.
Yayin da tilas Matawalle zai ji ciwon kayar da shi sosai, musamman la’akari cewa EFCC na jiran ya cire rigar da ke hana a kama gwamna, bisa zargin sa karkatar da wasu biliyoyin al’ummar Zamfara, ya sai maka-makan gidaje da filaye a Abuja.