Dan takarar gwamnan PDP a jihar Zamfara Dauda Lawal na zargin ‘yan kungiyar bangan gwamnati da kai wa tawagar kamfen din sa hari ranar Alhamis a Gusau.
Lawal ya fadi haka ne a takardar da sashen yada labarai na ofishin kamfen din sa ta fitar inda yake cewa wannan ba shine na farko ba da kungiyar ke kai wa tawagarsa hari a lokacin kamfen.
Gwamnan jihar Bello Matawalle ya kirkiro kungiyar ‘yan bangan domin kawar da aiyukan ‘yan jagaliya a jihar amma jami’yoyin PDP da NNPP na yawan zargin kungiyar da kai musu hari.
Ya ce haka kawai ‘yan kungiyar suka far wa tawagar motocin kamfen din sa hari har wani ya ji rauni.
Lawal ya ce ga dukan alamu gwamnati na so ta tada hankalin mutane kafin ranar zabe.
“A ranar 16 ga Maris ne kungiyar ‘yan bangan gwamnati suka kai wa twagar dan takarar gwamnan jihar Zamfara na jami’yyar PDP Dauda Lawal a titin Sani Abacha dake GRA a karamar hukumar Gusau.
“ ‘Yan bangan sun afka wa Dauda Lawal yayin da yake hanyar dawowa gida bayan Kamfen da yayi a wasu unguwannin jihar.
“Wannan shine karo na biyu da ‘yan bangan ke kai wa dan takarar hari a cikin wata daya.
“Aiyukkan da wannan kungiya ke yi ya saba wa doka domin doka ta Hanna kungiyar kama, cin zarafi, tursasa, muzgnawa, ta’addanci, tsarewa da duk Wani nau’i na azabtar da ‘yan jami’yyar adawa.
Lawal ya yi kira ga jami’an tsaron jihar da su samar da tsaro kafin zabe A jihar.
Discussion about this post