Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ta buƙaci a riƙa watsa zaman sauraron shari’ar ƙararrakin zaɓen da Atiku da kuma Tinubu su ka maka zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Ƙungiyar ta ce a lura a yanzu mafi yawan ‘yan Najeriya sun daina ganin darajar kotuna. Don haka watsa zaman sauraren shari’un nan biyu ya na da muhimmancin da yin hakan dai dawo wa da ɓangaren shari’a da kotuna martaba da ƙimar su a idon jama’a.
NBA ta bayar da wannan shawara ce a taron ta na Shugabannin Ƙungiya wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi, a ranar 23 Ga Maris.
Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi na Ƙasa, Yakubu Maikyau da Sakataren Ƙungiya na Ƙasa, Adesina Adegbite ne su ka saka wa takardar bayan taron hannu.
Sanarwar ta ce a yanzu jama’a da dama kwata-kwata sun daina ganin ƙimar kotuna, su na ganin ɓangaren shari’a ya na ta raba hanya daga turbar gaskiya. Saboda haka idan aka bada dama gidajen talabijin da jaridu su na watsa zaman shari’un ƙararrakin zaɓe, musamman zaɓen Shugaban Ƙasa, hakan zai dawo wa fannin shari’a martabar sa a idon jama’a.
Sanarwar ta ce ba a taɓa samun lokacin da jama’a su ka daina ganin darajar kotunan Najeriya ba, kamar wannan lokaci da mu ke ciki.
‘Yan takara dai waɗanda su ka faɗi zaɓuka daban-daban kama daga na shugaban ƙasa, gwamnoni, majalisar dattawa da ta wakilai ta ƙasa da majalisar dokokin jihohi, ku na ta tururuwar garzayawa kotu domin sun yi zargin an yi masu maguɗi.
Daga cikin mutanen farko da su ka garzaya kotu, akwai ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na LP.
Su biyun dai sun kowa ya nemi kotu ta ayyana cewa shi ne ya ci zaɓe, ko kuma kotu ta bayar da umarnin a sake zaɓe.
Discussion about this post