Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta sake zaɓe a rumfuna 13 da ke Mazaɓar Tudun Wada, Doguwa cikin Jihar Kano.
Mazaɓu ne da Alasan Doguwa ke wakilta, wanda Baturen Zaɓe ya bayyana ya yi nasara a zaɓen Majalisar Tarayya.
Sai dai kuma daga baya Baturen Zaɓe ya rubuta wa INEC wasiƙa cewa tirsasa shi aka yi ya bayyana cewa Ado Doguwa ne ya yi nasara.
Daga nan ne INEC ta soke zaɓen da aka yi a rumfunan guda 13, tare da kafa dalilin cewa tirsasa Baturen Zaɓe aka yi ya bayyana sakamakon zaɓe.
INEC ta hana Doguwa nasara a daidai lokacin da ya ke tsare ana tuhumar sa laifin kisan kai, banka wuta da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Baturen Zaɓe ya ce yawan ƙuri’un da aka soke a mazaɓun sun haura yawan bambancin ƙuri’un da ke tsakanin APC da NNPP.
Sai dai INEC ba ta bayyana ranar da za a yi zaɓen na cike ƙuri’un rumfunan zaɓen 13 ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa INEC ta ce Doguwa bai ci zaɓe ba, ‘yan da-tsiya-tsiya su ka tilasta Baturen Zaɓe ya ba shi nasara.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa daga Jihar Kano, Ado Doguwa, bai ci zaɓe ba.
INEC ta ce an tirsasa Baturen Zaɓe ne ya ambaci sunan Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara.
Doguwa dai ya na Majalisar Tarayya tun 2007, ana raɗe-raɗin kuma ya na tunanin ya shiga ya fita ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
INEC ta ƙi karɓar nasarar Doguwa kwanaki kaɗan bayan an gurfanar da shi kotu a Kano, bisa tuhumar sa da laifin kisa, banka wuta da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Babbar Kotun Tarayya ta Kano ta bayar da belin sa.
Baturen Zaɓe Ibrahim Yakasai ne ya bayyana sunan Doguwa wanda ya yi nasara da ƙuri’u 39,732, sai ɗan takarar NNPP, Salisu Abdulalhi ya zo na biyu da ƙuri’u 34,798.
INEC ta ce an tilasta baiwa Doguwa nasara a lokacin da aka yi wa Baturen Zaɓe barazana.
Wani bidiyo da wakilin mu ya gani wanda ake bayyana sakamakon zaɓen, an nuno Yakasai ya na magana kamar ya na kuka, ga jama’a kewaye da shi.
Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ruwaito cewa INEC ta cire sunan Doguwa daga jerin waɗanda su ka yi nasara.