Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da aka ce Buhari ya sha alwashin ba zai damƙa mulki a hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ba.
Kakakin Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa za a kitsa wannan ƙarya ba.
“Ta yaya Shugaban Ƙasa zai riƙa taya Tinubu kamfen, a yi zaɓe, ya yi nasara sannan kuma ya ce wai ba zai damƙa mulki a hannun sa ba?
Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa a ranar 29 Ga Mayu, kuma a ranar ce zai damƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Buhari ya ce ba zai damƙa mulki a hannun Tinubu ba.
Sai dai kuma cikin raddin da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Shehu ya ce yanzu haka kwamitin shirya miƙa mulki da Buhari ya kafa ya na nan ya na aiki.
Ya ƙara da cewa al’ummar Daura na can na ta shirye-shiryen karɓar ɗan su bayan ya kammala shekaru takwas ya na mulkin Najeriya.
“Shi kan sa ya ƙagara ya miƙa wa Tinubu mulki, ya tafi gida ya ji daɗin ritayar da ya yi.” Inji sanarwar da Shehu ya fitar.
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya shi ne Shugaban Kwamitin Miƙa Mulki hannun Tinubu, wanda Buhari ya kafa domin shirye-shiryen miƙa mulki.
“Abin da Sahara Reporters ke yi ba alheri ba ne kwata-kwata. Masu jaridar ba su yin adalci saboda sun ɗauki wani ɓangare saboda siyasa su na buga ƙarairayi da sharri da don ran su. Kowa ya san mai jaridar ya yi takarar shugabancin ƙasa, kuma ya faɗi zaɓe. Maimakon ya riƙa taɓo batutuwa masu alfanu, sai ya riƙa sayar da ƙarairayi, tsammanin sa duk abin da ya sayar wa jama’a za su fito da su saya.”
Shehu ya ce yanzu haka bayan babban kwamitin da aka kafa, an sake kafa wasu ƙananan kwamitocin har 13, kuma babu wasu matsalolin da ake fuskanta.
Discussion about this post