Kungiyar Ƙwadago ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai waɗanda ta ce lallai a cikin kwanakin ta gaggauta magance ƙarancin sabbin kuɗaɗe da kuma ƙaranci da tsadar fetur a faɗin ƙasar nan.
Kungiyar ta ɗauki wannan matsayar ce a cikin takardar bayan taron da shugabannin ta su ka fitar, wadda Shugaban NLC, Joe Anaero da Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja su ka sanya wa hannu a ranar Talata.
An fitar da takardar bayan Kwamitin Zartaswa na NLC ya gudanar da taron sa na ranar Litinin.
NLC ta ce rashin tsara shirin sauya launin kuɗi ya haifar da masifaffiyar tsadar rayuwa ga talakawan Najeriya.
Sannan kuma ta ce a cikin wannan mawuyacin hali an gudanar da abubuwa muhimmai uku a ƙasar nan, da su ka haɗa da zaɓen shugaban ƙasa da ma majalisar ƙasa, matsalar fetur da kuma sauya launin kuɗi.
“Saboda haka NLC ta yanke shawarar bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai cewa ta gaggauta magance matsalar sabbin kuɗi da kuma ta ƙarancin fetur.
NLC ta yi barazanar tafiya yajin aiki, idan aka cika kwanaki bakwai daga lissafin ranar 14 Ga Maris, to za ta tafi yajin aikin kai-tsaye.
Sannan kuma NLC ta yi wa Gwamnatin Tarayya da NNPC tofin tir, ganin har yau sun kasa yin wani hoɓɓasa domin magance tsadar fetur da kuma ƙarancin sa a faɗin ƙasar nan.
“NLC ta kuma yi Allah wadai da ƙarin kuɗin wutar lantarki, wanda aka yi ba tare da an sanar wa jama’a za a ƙara wa wutar lantarkin kuɗin ba.”
“Saboda haka daga yau NLC ta ƙudirta cewa duk lokacin da aka yi ƙarin kuɗin, to za su ruƙume ita da gwamnatin tarayya.