Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta bin umarnin Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke wanda soke wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗaɗe da CBN ta bayar.
A hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, ta kuma umarci a ci gaba da kashe tsoffin kuɗaɗe har zuwa 31 Ga Disamba, 2023.
Sai dai kuma kwanaki 10 kenan bayan hukuncin kotu, har yau CBN da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba su ce komai ba.
Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Maikyau, ya ce, “abin takaici ne Gwamnatin Tarayya da Bankin CBN sai abin da su ka ga dama su ke yi.”
NBA ta tuna wa Buhari irin yadda Kotun Ƙoli ta ragargaje shi, ta kira shi ɗan mulkin Fir’aunanci, saboda ya ƙi bin doka da hukuncin Kotun Ƙoli ta yanke kan batun soke wa’adin daina karɓar sabbin kuɗaɗe.
Idan ba a manta ba, Ƙungiyar Gwamnonin APC ta bayyana cewa CBN fashi da ƙwace ya yi wa mutane ya raba su da tsoffin kuɗaɗen hannun su.
PREMIUM TIMES ita ma ta yi kira a gaggauta tsige Gwamnan CBN, a damƙe shi, a garƙame shi a kurkuku.
Mashahuriyar jaridar nan da ta shahara wajen bankaɗo sahihan bayanan harƙalla, zamba da almundahana, PREMIUM TIMES, ta yi kira da cewa a gaggauta tsige Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
A cikin rubutun ta na uku da ta yi sharhi kan Emefiele, ta bayyana cewa ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli da Emefiele ya yi tantagaryar tsageranci ne, kuma babban cikas ne ga turbar dimokraɗiyya.
Sannan kuma jaridar ta bayyana cewa taƙaita adadin kuɗaɗen da za a riƙa cira a banki ko a ATM da POS, duk tauye haƙƙin da kundin tsarin mulki ya bai wa ‘yan Najeriya ne.
Sannan kuma sharhin ya nuna irin rashin mutuncin da Gwamnatin Tarayya da CBN su ka nuna, wato rashin fitowa su yi magana tun bayan da Kotun Ƙoli ta ba su umarnin dawo da karɓar tsoffin kuɗaɗen naira 200, 500 da kuma naira 1000, wanda kuma sun ƙi bin umarnin.
Idan za ta tuna, PREMIUM TIMES ta sha yin kiraye-kirayen cewa a cire Emefiele daga gwamnan CBN, wanda ta fara tun farkon fitowar sa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, wanda ya wayance, ya janye tun kafin a kai ga zaɓen fidda-gwani.
“Babban abin damuwar mu ba wai hukuncin da kotun ta yanke ba, a’a, ƙin bin umarnin kotu shi ne babban abin damuwa, kuma babbar kotu ta ƙasa baki ɗaya, wato Kotun Ƙoli.
“Dalili kenan mu ke yin kira da a tsige Emefiele, a damƙe shi, a gurfanar da shi kotu kuma a garƙame shi.”