Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar ya ce laifin Buhari ne da ƙasar nan ta tsinci kan ta a jerin ƙasashen da ke fama da gigitaccen tattalin arzikin ƙasa.
Atiku ya ce idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023, zai hanzarta wajen ceto tattalin arzikin Najeriya daga cikin kwatamin da Buhari ya jefa shi.
Atiku ya yi wannan bayani ne cikin wata sanarwa bayan da aka fitar da alƙaluman ɗimbin bashi da koma bayan hada-hadar bunƙasa tattalin arziki, wanda Najeriya ta tsinci kan ta a ciki.
Cikin makon jiya ne wata ƙungiya mai ƙididdigar ɗora ƙasashe bisa mizanin awon koma bayan tattalin arzikin ƙasa ya ce Najeriya ta samu gagarumin koma baya ta fuskar matsalar kuɗaɗe da ɗimbin basussuka.
Mizanin awon ya nuna Najeriya za ta ci gaba da fuskantar wannan mawuyacin hali, a matsayin ta babba a tattalin arzikin ƙasashen Afrika.
Zazzafa Daga Atiku Zuwa Ga Buhari: Mugun zarin ka na rashin ƙyamar ciwo bashi ko a ina ne ya sa ka kasa rage giɓin kasafin kuɗi a duk shekara. Sai ka ɓuge wajen ɗibga babban kuskuren rika ciwo bashin Bankin CBN. To yanzu ga shi nan ka kai ƙasar ka baro.”
“Saboda haka ni idan aka ba ni damar saisaita tattalin arzikin Najeriya. Ida da idanu garau, ba makahon da ko ɗan jagora ba shi da shi ba ne. Zan yi ƙoƙarin tabbatar da dawo da tattalin arzikin Najeriya ciki hayyacin sa.” Inji Atiku.
Discussion about this post