Alƙaluman ƙididdigar yawan waɗanda su ka karɓa ɗin ya kuma nuna cewa akwai rajistar mutum 6,259,229 waɗanda har yanzu ba su karɓi katin shaidar rajistar zaɓen su ba.
Kashi 93.3 na waɗanda su ka yi rajista dai kenan duk sun karɓi katin shaidar rajistar su, wanda aka rufe karɓa a ranar 5 ga Fabrairu.
Kashi 6.7 kaɗai ne waɗanda su ka yi rajistar katin zaɓe, amma kuma ba su karɓa ba.
Idan aka kwatanta da na zaɓen 2019 wanda kashi 86.3 ne su ka karɓi kati, za a ga cewa waɗanda su ka karɓa a 2023 sun fi yawa kenan.
A zaɓen 2015 kuwa kashi 81.2 ne na waɗanda su ka yi rajista su ka karɓi katin su.
Waɗanda su ka yi rajista a jihar Bauchi ne su ka fi karɓar na su da kashi 99, sai Anambra kashi 98.8 sai kuma Katsina kashi 98.4.
Jihohin Oyo, Ogun, Edo, Ondo da Legas ne su ka fi yawan waɗanda ba su karɓi na su katin rajistar ba, da kashi 81.5, 84.3, 84.7, 85.1 da kuma 86.9 a jere.
Jihar Legas ce ta fi yawan waɗanda su ka karɓi katin rajsita, har mutum 6,214,970, sai Kano mai mutum 5,594,193 da kuma Kaduna mai mutum miliyan 4,164,473.
Haka kuma jihar Legas ta fi sauran jihohin filin katin zaɓen da ba a karɓa ba, har guda 845,225, sai Oyo mai 515,253 da kuma Ogun mai 410,281.