Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen APC ta yi zargin cewa PDP da LP su na neman umarnin kotu ta hana ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai Festus Keyamo ya fitar a ranar Litinin, ya ce Dokar Zaɓe ta haramta wa kotu dakatar da zaɓe ko wasu ayyukan da su ka jiɓinci zaɓe a Najeriya.
Ya ce hasalallun jam’iyyyun ba za su iya tunkarar kotu ta ba su iznin dakatar da ayyukan zaɓe.
Kama daga PDP har LP dai ƙorafe-ƙorafen da su ke yi ya samo asali ne daga yadda ake tattara sakamakon zaɓe a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe, Abuja.
Sun jajirce sun ce tilas sai INEC ta riƙa loda sakamakon zaɓe a manhajar ganin sakamakon zaɓe, wato iRev.
Shugaban INEC dai ya fito ya ce zargin aringizon ƙuri’u a zaɓen Ekiti ba gaskiya ba ne.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi watsi da zargin da PDP ta yi kan zaɓen Jihar Ekiti, wanda jam’iyyyar ta ce an yi aringizon ƙuri’u.
APC ce ta yi nasara a Jihar Ekiti, kuma sakamakon zaɓen jihar ne aka fara bayyanawa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe a Abuja, a ranar Lahadi.
A ranar Litinin kuma sai ejan ɗin PDP a cibiyar, Dino Melaye ya Yi kira da a soke sakamakon zaɓen Ekiti, wanda ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri’u.
Melaye tun da farko ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u 800 a zaɓen jihar Ekiti.
Shi da ɗayan ejan ɗin PDP, Emeka Iheodia, sun fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe da ke Abuja, bayan da Shugaban INEC ya ƙi biya masu buƙatar su.
Daga baya Yakubu ya maida raddin cewa babu wani abu mai kama da aringizon ƙuri’u a zaɓen Jihar Ekiti.
Ya ce babu wani aringizon ƙuri’u domin ejan ɗin jam’iyyu a Ekiti sun sanya hannun amincewa da sakamakon zaɓen.
Yakubu ya ce alƙaluman da ejan ɗin PDP ya bayyana ba daga INEC ya same su ba.
Ya ce INEC na da adadin mutum 315,058 waɗanda aka tantance, sannan daga ciki halastattun ƙuri’u su 308,171 ne. Sai kuma ƙuri’un da aka ƙi amincewa da su har 6,301.
Daga nan ya yi kira ga jam’iyyu su tuntuɓi INEC domin samun sahihin adadi, idan har wanda su ke da shi ya sha bamban.
A Jihar Legas ma PDP ta ƙi amincewa da sakamakon yawan ƙuri’un Peter Obi a Legas.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta amince da sakamakon yawan ƙuri’un da jam’iyyar LP ta Peter Obi ta samu a Jihar Legas ba.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Legas, Tunji Shelle wanda kuma shi ne ejan ɗin PDP wurin tattara sakamakon zabe a Yaba, Legas, ya ce “an yi ƙumbiya-ƙumbiya gabaɗayan aikin tattara ƙuri’un.”
“Ban amince da sakamakon zaɓen ba, kuma na ɗauki wannan matsaya ce a madadin jam’iyyar da na ke wakilta, PDP.” Haka Shelle ya bayyana wajen tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin.
“Ban amince da sakamakon da LP ta samu ba, ba wai don ba mu yi nasara ba. Amma saboda an saye waɗanda aka saye aka yi mana ƙumbiya-ƙumbiya.”
Peter Obi na LP dai ya lashe yawan ƙuri’un jihar Legas har 582,454, shi kuma Bola Tinubu na APC 572,606.
Atiku Abubakar na PDP ya samu 75,750.
“Ba na jin INEC ta bayar da kyakkyawan horon aikin zaɓe ga ma’aikatan wucin-gadin da ta ɗauka. Saboda a gaskiya ba mu shirya wa fara aiki da na’urar tantance masu rajistar zaɓe ba, wato BVAS. Saboda a wurin tantancewar ne ake yin amaja. Da yawan sakamakon zaɓen duk ba a ma loda su a BVAS ɗin. Amma haka aka fitar da sakamako.”
Ya ce kamata ya yi BVAS ya tsaftace aikin zaɓe, amma maimakon haka, sai ma ya ƙara maida hannun agogo baya.