Shugaban INEC ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa za a gudanar da sahihin zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa za ta gudanar da sahihin zaɓe kuma wanda zai kasance karɓaɓɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya ƙara jaddada haka, lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Wakilin Sa-ido na Kungiyar Ƙasashe Rainon Ingila (Commonwealth), ranar Litinin a ofishin sa da ke Hedikwatar hukumar a Abuja.
“Tuni INEC ta fahimci muhimmancin gudanar da sahihin zaɓe, ba ma a Najeriya kaɗai ba, har a nahiyar Afirka baki ɗaya.
“Gudanar da zaɓe a Najeriya babban aiki ne. Amma kamar yadda na ce, nauyin gudanar da wannan gagarimin aiki ya na a wuyan mu.
“Muhimmancin gudanar da sahihin zaɓe bai tsaya wajen samar da wanzuwar zaman lafiya da nagartacciyar gwamnati kaɗai ba. Tasirin sahihin zaɓe a Najeriya ya shafi har sauran ƙasashen Yammacin Afirka.
“Ina tabbatar maku da cewa ba za mu taɓa yarda mu bai wa Najeriya da duniya kunya ba.” Haka Yakubu ya shaida wa Shugaban Wakilan Sa-idon Kasashe Rainon Ingila, Thabo Mbeki, wanda tsohon Shugaban Ƙasar Afrika ta Kudu ne.
Yakubu ya kuma jinjina wa irin gudummawar da ƙungiyar ta ke bayarwa ta hanyar turo wakilan sa-ido masu lura da zaɓuɓɓukan da INEC ke gudanarwa a Nijeriya.
Ya ce Najeriya ta amfana sosai daga shawarwarin da ƙungiyar ke bayarwa a zaɓuɓɓukan da Najeriya ta gudanar a baya.
Da ya ke jawabi, Mbeki ya ce maƙasudin zuwan su Najeriya shi ne sa-ido da lura da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya gudana, sannan kuma a ƙarshe su bayar da rahoto a rubuce.
“Wannan shi ne zai kasance zaɓe na bakwai tun bayan samun ‘yanci a Najeriya. Zaɓen ya na da muhimmanci ga ita kan ta da kuma Afirka baki ɗaya.
“Dalili kenan mu ke zuwa domin ganin yadda zaɓe ke gudana, mu koma mu kai rahoto. Amma mu na da yaƙinin cewa za a gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana.”
Discussion about this post