Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwana al’ummar Najeriya, masu daraja! Hakika nayi bincike lokaci mai tsawo a cikin Alkur’ani Mai girma da littafan tafsirai daban-daban, musamman akan kissar Bani Isra’ila, Annabi Shamwilu da Daluta; da kissar Annabi Musa, da kissar Annabi Dawud; da kuma Hadisan Manzon Allah (SAW) da littafan addinin Musulunci wadanda suka yi magana akan shugabanci da muhimmancinsa da kuma siffofin irin shugaban da ya kamata ya shugabanci al’ummah domin a samu ingantaccen shugabanci nagari wanda zai amfani al’ummah baki daya, kuma kowa yaji dadi, a samu zaman lafiya, hadin kai da cigaba mai dorewa. Na binciki littafai irin su Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Al-Mawardi da Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Abu Ya’ala da As-Siyasah Ash-Shar’iyyah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah, da sauran littafai muhimmai, ire-irensu, wadanda suka yi magana akan shugabanci da siffofin shugaba nagari.
A cikin binciken da nayi, alhamdulillahi, na fitar da siffofi guda ashirin (20), wadanda Allah da Manzonsa (SAW) da kuma malamai suka bayyana; siffofin da ya kamata ace duk shugaban da zai shugabance mu yana da su.
Shawarwari ne da jan hankali, wadanda addinin Musulunci ya bai wa al’ummah, wadanda ya kamata suyi la’akari da su, musamman wurin zaben shugaba, in dai har suna son samun walwala da ci gaba a cikin al’ummarsu.
Wadannan shawarwari hakika, idan al’ummah ta bisu wurin zaben shugabanni, to zasu yi nasara kuma suji dadi. Amma kuma idan al’ummah suka ki bin wadannan shawarwari, suka bi son zuciyarsu, to tabbas sai sun yi dana-sani game da sha’anin lamarin shugabancinsu.
Saboda sha’anin shugabanci ba abun wasa bane da zamu yi wasa ko sakaci da shi, ko kuma mu takaita shi akan la’akari da wata jam’iyyah ta siyasa, ko kuma la’akari da yaren shugaba ko kabilarsa, ko yankin da ya fito, ko kuma mu mayar da shi akan tafarki na karba-karba, wanda duk wadannan hanyoyi ne na shirme da shiririta! A sha’anin shugabanci, cancanta kawai ake bi da dacewa. Wanda ya cancanta kuma ya dace, shine ya zama wajibi mu zaba. Idan muka kuskura muka zabi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to lallai mu sani, zamu sha wahala anan duniya, kuma lahira zamu amsa tambayoyi a gaban Allah, akan duk wata irin gudummawa da muka bayar wurin dora shugaban da muka san bai dace ba akan al’ummah!
Ya ku jama’ah! Ku sani, lallai sha’anin shugabanci ya wuce haka, kuma yafi karfin haka. Bai kamata mu takaita maganar shugabanci da wani son zuciya ba, kasancewar duk wanda zai shugabance mu, lamarin rayuwar mu gaba daya ya rataya ne akan yanayin irin shugabancin da yayi muna.
Duk wanda ya zama shugaba a cikin mu, ya zama wajibi ya kare addininmu, da rayukanmu, da dukiyoyinmu, da hankalin mu da nasabar mu ko dangantakar mu, tare da kokarin samar muna da sauran ababen more rayuwa, domin rayuwar mu ta inganta, muji dadin bautawa Allah cikin hayyacinmu.
To tun da haka ne, kenan ya zama dole, kuma wajibi mu san wanene zai shugabance mu. Ga siffofin shugaban da ya kamata ya shugabance mu kamar haka:
1. Dole ne duk shugaban da zamu zaba ya zamanto yana da ilimi, yana da hikimah, yana da hangen nesa da kwarewa (Knowledge, wisdom, vision and competence).
2. Dole ne shugaba ya zamanto mai karfi a jiki, mai kazar-kazar, mai kwarjini (Power/Strength).
3. Dole shugaba ya zamanto yana da hikimah wurin zartar da hukunci, domin ya iya zartar da hukunci ingantacce (Sound Judgement).
4. Dole shugaba ya zamanto mai hakuri, mai juriya, sannan mai yafiya (Patience, Tolerance and forgiveness).
5. Dole shugaba ya zamanto adali kuma marar nuna banbanci tsakanin ‘yan kasa (Justice and fairness).
6. Dole ne shugaba ya zamanto yana da fasaha, hikimah da basirah wurin isar da sako zuwa ga al’ummah (Communication skills).
7. Dole ne shugaba ya zama mai tsoron Allah (Piety/At-Taqwah).
8. Dole shugaba ya zama mai saukin kai, ba mai kafiya ko kangara ba, mai kwarjini da kazar-kazar sannan mai cikakken hankali da tunani (Simplicity, emotional and spiritual intelligence).
9. Dole shugaba ya zamanto mai gaskiya ba abun zargi ba (Truth).
10. Dole shugaba ya zama lafiyayye; mai lafiyar kwakwalwa da ruhi da jiki (Sound and good health/Soundness in mental and physical condition).
11. Dole ne shugaba ya zamanto mai amanah da iya rikon amanah kuma mai mutunci (Trust and Integrity).
12. Dole be shugaba ya zama mai tuntuba kafin ya zartar da wani abu (Consultation).
13. Dole ne shugaba ya zamanto mai iya zartar da hukunci bayan ya tuntubi masu ilimin fannin, ba tare da tsoro ko fargabar kowa ba (Decisiveness/Decision making ability after consultation).
14. Dole ne shugaba ya zamanto mai dogaro tare da tawakkali ga Allah, ya zamo jarumi, marar tsoro, kuma mai cikakken yakini (Dependence on Allah, courage, bravery and confidence).
15. Dole ne shugaba ya zamanto mai sadaukarwa wurin kowane lamari (Spirit of sacrifice).
16. Dole shugaba ya zama mai cika alkawari, kuma mai mutunta alkawurran da ya daukar wa al’ummah, ba mai karya alkawari ba (Honouring the pledge).
17. Dole ne shugaba ya zamanto mai kyauta, mai alkhairi, karimi ba marowaci ba (Generosity).
18. Dole ne wanda za’a zaba ya zamanto shugaba ya kasance zai iya, kar mu zabi wanda muka san cewa ba zai iya ba, ko dukkanin alamu sun nuna ba zai iya ba (Capacity to govern).
19. Dole ne shugaba ya zama yana kokarin binciken kan sa da kuma dukkanin ma’aikatansa. Dole ya zama mai tsantseni da kula da dukiyar baitul mali. Kar mu zabi shugaban da muka san cewa zai yi kokarin arzirta kan sa da dukiyar al’ummah. Kuma kar mu yarda mu dora almubazzari akan dukiyar kasa (Accountability/Ihtisab).
20. Dole ne shugaba ya zamanto mai fada da cikawa; wanda zai yiwa al’ummah aiki, ba surutun banza da yawan magana ba. Kar mu dora wanda muka san mai fada ne kawai, amma ba zai cika ba (Action not just words).
Ya ku ‘yan uwa! Wadannan kadan kenan daga siffofin shugaba nagari da ya kamata mu zaba a wannan zabe mai zuwa da ikon Allah. Tun daga zaben shugaban kasa har zuwa na Gwamnoni; kar mu yarda muyi sake, ko kuma mu zabi shugaban da muka san bai cancanta ba ko bai dace ba.
Ku sani, ana maganar Najeriya ce fa, kasar mu ta gado; kasar da muke so kuma muke kauna. Kasar da bamu da wani wurin zuwa idan ba ita ba. Kasa mai arziki, wadata da yalwa, amma rashin samar da shugabanci nagari yasa muna ta shan wahala. Kasa mai dauke da al’ummomi har mutum sama da miliyan dari biyu. Kasa irin wannan, wallahi bai kamata mu kasance masu sakaci wurin zabar mata shugabanni ba. Ko kuma mu rungume hannu, muna kallo a rinka dora muna shugabannin da mun san ba zasu iya ba, ko kuma basu dace ba, basu cancanta ba!
Ya zama wajibi mu zabi shugabanni nagari, wadanda suke son mu muke son su, suke yi muna addu’a muke yi masu addu’a. Ba shugabannin da zasu rinka zagin mu ba muna zaginsu, suna la’antarmu muna la’antarsu.
Don haka, muna kira ga al’ummah baki ɗaya cewa, in dai har da gaske ne muna son Allah ya taimake mu, kasar mu ta gyaru, to sai kowa ya tashi tsaye wurin yin abun da ya kamata wurin zaben shugaba nagari, tare da yin addu’ar Allah ya kawo muna sauki, ya fitar da mu daga tsananin da muke ciki.
Mu gyara halayenmu da dabi’unmu, kuma muyi ta addu’a da rokon Allah ya arzurta mu da shugaban ƙasa nagari a wannan zaɓe mai zuwa; shugaba mai tausayi, mai fahimta, mai son al’ummah, mai kwarin jiki da lafiyar jiki da ta hankali, mai son haɗin kan ƙasa, mai kishin Najeriya da ‘yan Najeriya da arewa da kowane yanki baki daya; mai saukin kai da karɓar shawara, sannan kuma kwararre wurin iya mulkin ƙasa, wanda ba dan koyo ba kuma ba sabon shiga ba. Muyi fatan irin wannan shugaba Allah ya bashi nasarar cin zabe a wannan zabe mai zuwa, kuma Allah ya bashi nasara wurin aikata alheri a cikin shugabancinsa.
Sannan game da abunda yake faruwa a kasarmu, game da canjin kudi a halin yanzu, ina kira da muyi hakuri. Mu sani, babu wani gyara da za’a yi a duniya, kuma a ko’ina ne, ba tare da an sha wahala ba! Mu bincika da kyau mu gani, duk wata kasa a duniya, mu koma mu bibiyi tarihin manyan kasashen duniya, kafin su kai matsayin da suke akai a yau, sai da suka sha wahala sosai!!
Kai a wasu kasashen ma, wasu jinin su suka ba da, balle wai don muna shan wahala saboda canjin kudi. Malamai magana fa ake yi ta gyaran Najeriya da izinin Allah da iyawarsa!
Muyi hakuri har ayi zabe lafiya a gama lafiya. Kar mu yarda a zuga mu, ko a harzuka mu, ko ayi amfani damu, mu tayar da hankali, ko muyi hargitsi, ko muyi wata zanga-zanga ko hayaniya. Mu sani, komai mai wuce wa ne da yardar Allah, kuma da izinin Allah, wata rana sai labari. Amma dai muyi kokari mu zabi shugaba nagari a ranar zabe, wanda da ikon Allah, Allah zai yi amfani da shi wurin taimakon Najeriya da taimakon dukkanin ‘yan kasa baki daya.
Kar mu yarda mu biye wa ‘yan wasu yanki masu kone-kone da kashe-kashe da tayar da hankula da zanga-zanga, domin mu irin wannan aiki sam ba tarbiyyar mu bace.
Sannan kar mu yarda mu biye wa wasu Gwamnoni masu kokarin harzuka mu da zuga mu akan muyi tawaye, da sunan wai saboda talakawa suke yi, alhali duk wani mutum mai hankali yasan ba domin talakawa suke yi ba, domin kawunansu kawai suke yi. Kar mu taba yarda da duk wani abu da zai tayar da hankalin kasarmu mai albarka!
Sannan mu sani, duk mai hankalin da ya kai shekarun zabe, tabbas yasan dacewa da cancantar wanda ya kamata ya zaba, kar ka yarda da wai wani yasa ka zabi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, domin mun san irin wahalhalun da muka sha, da irin bala’in da Allah ya jarabe mu dashi. Kuma masu hikimah sun ce idan kunne yaji to gangar jiki ya tsira!
Kuma idan wani yasa ka zabi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to ka sani, a ranar da zaka amsa tambayoyi a gaban Allah, wannan mutum ko waye shi baya wurin bare har ya cece ka daga azabar Allah!
Wassalamu Alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya, wanda yake Mamba a kwamitin Matasan Malamai masu rajin samar da shugabanci nagari. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.