Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na naira 200 daga yanzu har zuwa 10 ga Mayu.
A cikin jawabi da shugaba Buhari yayi ranar Alhamis, Shugaban kasa ya ce ya umarci babban bankin kasa ta wadata bankuna da sabbin takardun kuɗaden don ya ishi jama’a.
Bayan haka ya umarci yan Najeriya su yi hakuri da gwamnati su bi doka cewa ba a bullo da wannan tsari ba don a muzguna wa mutane.
” Daga yanzu za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na naira 200 tare da sabbin takardun kuɗin. Sai dai kuma za a dai ma amfani da su ne daga ranar 10 ga Mayun 2023.
Buhari ya ce wannan kafa da gwamnati ta ɗaga bai hada da takardun kuɗi na naira 500 da naira 1000 ba.
Discussion about this post