Zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a yau Asabar, ya kai har cikin dare ana yi wata rumfar zaɓe a Kano.
Wakilin mu da ya zanta da wani aminin sa maƙaucin rumfar zaɓen, ya tabbatar masa da cewa ya isa rumfar zaɓen tun ƙarfe 9:17 na safe, amma bai samu jefa ƙuri’a ba sai 9:03 na dare.
Rumfar zaɓen dai ta na Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Gwale, Kuntau Science Acadamy, wajen Afforestry, Kano.
Ga yadda ta kasance a hirar wakilin mu da wanda ya dangwala ƙuri’a cikin dare.
“Na je rumfar zaɓe da misalin ƙarfe 9:17 na safe.
“Malaman Zaɓe sun zo da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
“Na jefa ƙuri’a ta da misalin ƙarfe 9:03 na dare.
“Sunan Rumfar Zaɓen Zainab Vision PU, Kuntau Science Academy, wajen Afforestry, Kano, cikin Ƙaramar Hukumar Dala.
“Gaskiya yin daren mu ba ya rasa nasaba da ƙarancin ma’aikatan zaɓen, domin akwatin da na yi zame gaba ɗaya mutane 600 ne waɗanda za su jefa ƙuri’ar su.
“Yanzu dai na baro wajen zaɓen ba tare da an gama ba. Ban sani ba zuwa yanzu da na baro ko an gama. Amma lallai na baro jama’a aƙalla sama da mutum 80 ba su ma jefa ba.
“Na isa gida ƙarfe 10 na dare.”