Ɗan takarar shugaban kasa na LP ya doke Bola Tinubu na APC a karamar hukumar Ikeja, inda nan ne mazabar Tinubu ya yake.
Sakamakon zaɓen da aka bayyana na karamar hukumar Ikeje, ya nuna Obin LP ya samu Kuri’u LP 30,004, shi kuma Tinubu na APC ya samu Kuri’u 21, 267.
Ita ko jam’iyyar PDP ƙuri’u 2000 kacal ta samu a wannan ƙaramar hukuma.
Sai dai kuma a Badagry, Tinubu ne yayi nasara a zaɓen. Ya nunka Kuri’un da Obi ya samu har sau biyu. APC ta samu Kuri’u 31903, LP 10956, PDP kuma ta samu 6024.
Discussion about this post