Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya bayyana cewa hukumar ta kama sabbin takardun kuɗi na naira miliyan 32 a Legas, waɗanda ake zargin za a yi harƙallar siyan ƙuri’u ne da su.
Hukumar ta ce tuni an tasa ƙeyar wanda aka kama kuɗin a hannun sa zuwa hukumar domin yi masa tambayoyi.
Haka kuma rundunar ƴan sandan jihar Ribas ta kama wani ɗan majalisar tarayya da $498,100 da takarda kunshe da jerin sunaye mutanen da ake zaton zai baiwa kuɗin ne domin siyan ƙuri’u a zaɓen gobe.
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya hori ma’aikatan hukumar su ba mara ɗa kunya sannan su jajirce wajen aikin su a lokacin zaɓe.
Ya kara da cewa an tura jami’an EFCC ɗin ko ina domin sa ido domin dakike siyan ƙuri’u a lokacin zaɓe.