Ɗan takarar shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar, ya lallasa babban abokin takarar sa na APC, Bola Tinubu a zaɓen jihar Osun.
Atiku ya lashe zaɓe a kananan hukumomi 20 inda ya samu Kuri’u 354,366. Shi kuma Bola Tinubu na APC ya samu Kuri’u 343,945 a kananan hukumomi 10 na jihar.