Ɗan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi nasara a zaɓen shugaban kasa a jihar Sokoto.
Bisa ga alkaluman da baturen zaɓe ya bayyana ranar Litinin a garin Sokoto, Atiku ya samu Kuri’u 288,679, APC kuma ta samu Kuri’u 285,444.
Baturen zaɓe Farfesa Kabiru Bala na Jami’ar ABU, ya kara da cewa jam’iyyar NNPP ta samu Kuri’u
1,300 ne kacal sai LP da ta samu kuriu 6,568.
Accord Party (A) ta samu 115, Action Alliance (AA) 110, AAC 128, ADC 486, ADB 1,105, APGA 808
APM 273, APP 219, BP 126, NRM 681, PRP 324, SDP 120, YPP 175, ZLP.
Discussion about this post