Dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar PDP Atiku Abubakar ya kada dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar LP Peter Obi a karamar hukumar Itu dake jihar Akwa-Ibom.
Bisa ga sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar ranar Lahadi ya nuna Atiku ya samu kuri’u 7,276 sannan Obi 6,001.
Hukumar ta Kuma ce sakamakon zaben Wanda aka tattare da ga gundumomi 10 ya nuna cewa jami’yyar APC ta samu kuri’u 4,134.