Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi nasara a zaɓen shugaban kasa na jihar Katsina.
Duk da ko cewa kuma har ita ce jihar shugaba Muhammadu Buhari, hakan bai sa Katsinawa sun raga wa Buhari sun fidda shi kun ya ba, sun rattaba wa Atiku kuri’un su.
A sakamakon da malamin zaɓe ya bayyana a Katsina, Atiku ya samu kuri’u 489,045, sha kuma Bola Tinubu na APC ya samu Kuri’u 482, 283.
Kwankwaso na NNPP ya samu Kuri’u 69,386.
Sai dai kuma Tinubu ne ya fi lashe kuri’u a kananan hukumomin jihar. Ya lashe ƙananan hukumomi 21, Atiku ya lashe 13 amma kuma yawan kuri’un da ya samu sun fi yawan na Tinubu.