Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, wanda ya na ɗaya daga cikin Gwamnonin PDP biyar da su ka ƙi goyon bayan takarar Atiku Abubakar, ya yi nasarar ciwo wa Bola Tinubu na APC akwatin Mazaɓar Gwamna.
A akwatin zaɓe mai lamba 01 a Mazaɓa ta 11 da ke kan titin Abayomi cikin Ibadan, APC ta samu ƙuri’u 104, LP 82 PDP kuma 27.
Sai dai kuma PDP ta lashe zaɓen sanata da ƙuri’u 82, inda APC ta samu 79.
A Rumfar Zaɓen Mataimakin Gwamnan Oyo Adebayo Lawal, can ma APC ce ta lashe zaɓen da ƙuri’a 236, PDP kuwa ta samu 114.
A nan ma PDP ce ta lashe takarar Sanata da ƙuri’u 127, APC 123.
A Abuja kuwa, Jam’iyyar Peter Obi ta ragargaji su O’o da O’o a rumfunan zaɓen kewayen Fadar Shugaban Ƙasa.
Jam’iyyar LP wadda Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa, ta lashe zaɓen rumfar zaɓe ta 12 da ke Fadar Shugaban Ƙasa, amma dai wannan jaridar ba ta kai ga samun sauran sakamakon zaɓen ba tukunna.
Peter Obi ya lashe yawancin rumfunan zaɓen kewaye da fadar ta Shugaban Ƙasa a Abuja.
Runfa mai lamba 022, Obi ya samu ƙuri’u 174, PDP 78, APC kuma 71.
Runfa mai lamba 021 kuwa Obi na LP ya samu 190, APC 87, PDP 70.