Yankin Arewa maso Gabas dai ya fi sauran yankuna yawan jihohi da yawan al’umma. Kuma shi ne ya fi sauran yankunan samun yawan ƙuri’u.
A zaɓen 2019 dai Buhari ya fi Atiku yawan ƙuri’u a waɗannan jihohi. Duk da dai Atikun a garzaya kotu ya ce a can ne aka yi masa maguɗi.
A 2019 Buhari ya samu ƙuri’u 5,995,751 a waɗannan jihohi bakwai. Shi kuma Atiku ya samu miliyan 2,280,465.
Buhari ya samu ƙuri’u 1,464,768 a Kano. A Katsina a 2019 kuma ya samu 1,232,133. A Kaduna Buhari ya samu 993,445, sai kuma Jigawa 784,738.
To sai dai kuma a wannan zaɓe na 2023, Kwankwaso ya fito shiyya ɗaya da Buhari, duk da dai Buharin ba ya cikin ‘yan takara. Sannan kuma a shiyyar akwai ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP, Datti Baba Ahmed. Kwankwaso na da magoya baya masu ɗimbin yawa a Kano da jihohin da ke maƙwautaka da Kano ɗin.
Jihar Kaduna ce ta fi bai wa Atiku ƙuri’u masu yawa a 2019, guda 649,612. Atiku ya shaida wa kotu cewa an yi wa APC aringizo sosai a Katsina, shi ya sa aka bar PDP da ƙuri’u 308,051 kacal, ita kuwa APC miliyan 1.2.
To a yanzu PDP na sa ran samun ƙuri’u da dama a Jigawa, Katsina, Sokoto, Kebbi da Kaduna. Duk da matsalar rabuwar da PDP ta yi a Kano, ana sa ran za ta samu ƙuri’u idan aka yi la’akari da irin ganin cewa akwai masu goyon bayan Atiku sosai a Kano. Amma kuma wasu na ganin daga PDP har APC ba za su fi Kwankwaso yawan ƙuri’u a Kano ba.