Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya lashe dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar Ekiti da ƙuri’u 201,486. Shi kuma Atiku Abubakar na PDP ya samu 89,554. Peter Obi na LP kuma ya samu 11,397.
Wani abin dubawa shi ne Tinubu bai samu yawan ƙuri’un da Buhari ya samu a Ekiti a zaɓen 2019 ba, inda a wancan lokacin Buhari ya samu 219,231.
Shi ma Atiku bai yi ƙoƙari ba a 2023, idan aka kwatanta da cewa ƙuri’u 154,034 Wazirin Adamawa ya samu a 2019.
A jihar Filato kuwa, Peter Obi ya bi Daraktan Kamfen ɗin Tinubu har gida a Filato, ya kunyata shi.
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, wanda shi ne Daraktan kamfen ɗin TInubu 2023, ya kwashi buhun kunya har gida, inda Peter Obi ya lashe sakamakon zaɓen rumfar sa da akwatin sa, a jihar Filato.
Lalong ya yi zaɓe a Unit 05, Kurumbo Ward B a Ƙaramar Hukumar Shendam.
Bayan an kammala ƙidaya, LP ta samu 104, APC 88 sai kuma PDP 8 a zaɓen shugaban ƙasa.
Amma a zaɓen sanata APC ce ta samu nasara a akwatin zaɓen da ƙuri’a 143, PDP 39, sai LP mai 14 kacal.
A Jihar Oyo kuwa, Gwamna Makinde ya ya yi wa Atiku ‘anti-party’, ya danƙara wa Tinubun APC ƙuri’u.
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, wanda ya na ɗaya daga cikin Gwamnonin PDP biyar da su ka ƙi goyon bayan takarar Atiku Abubakar, ya yi nasarar ciwo wa Bola Tinubu na APC akwatin Mazaɓar Gwamna.
A akwatin zaɓe mai lamba 01 a Mazaɓa ta 11 da ke kan titin Abayomi cikin Ibadan, APC ta samu ƙuri’u 104, LP 82 PDP kuma 27.
Sai dai kuma PDP ta lashe zaɓen sanata da ƙuri’u 82, inda APC ta samu 79.
A Rumfar Zaɓen Mataimakin Gwamnan Oyo Adebayo Lawal, can ma APC ce ta lashe zaɓen da ƙuri’a 236, PDP kuwa ta samu 114.
A nan ma PDP ce ta lashe takarar Sanata da ƙuri’u 127, APC 123.
A Abuja kuwa, Jam’iyyar Peter Obi ta ragargaji su O’o da O’o a rumfunan zaɓen kewayen Fadar Shugaban Ƙasa.
Jam’iyyar LP wadda Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa, ta lashe zaɓen rumfar zaɓe ta 12 da ke Fadar Shugaban Ƙasa, amma dai wannan jaridar ba ta kai ga samun sauran sakamakon zaɓen ba tukunna.
Peter Obi ya lashe yawancin rumfunan zaɓen kewaye da fadar ta Shugaban Ƙasa a Abuja.
Runfa mai lamba 022, Obi ya samu ƙuri’u 174, PDP 78, APC kuma 71.
Runfa mai lamba 021 kuwa Obi na LP ya samu 190, APC 87, PDP 70.