Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa ta yi kira ga ‘yan Najeriya su yi amfani da damar da su ka samu ta ranar 25 Ga Fabrairu mai zuwa su maye gurbin gwamnatin APC ta hanyar zaɓen PDP.
PDP ta ce babu wani dalilin da zai sa a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, domin shi ne da kan sa ke tutiyar cewa shi ya ɗora APC kan mulki, har ta jefa ƙasar nan cikin mawuyacin halin ƙuncin da ake fama da shi a yanzu.
Rundunar yaƙin ta ce babu abin da ya kamaci gwamnatin APC sai a yi mata munmunan kayen da ba za a sake jin motsi, minshari ko gurnanin jam’iyyar ba.
Wannan bayani ya na cikin wata sanarwar da Kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya fitar, a ranar Talata, a Abuja.
Yayin da ake ta ƙoƙarin ganin zuwan ranar zaɓen shugaban ƙasa, ko a ranar Talata ɗin sai da wani hadimin Atiku Abubakar ya yi zargin cewa “Gwamnonin APC na ƙoƙarin haddasa tunzirin da zai iya dagula Najeriya.”
A wancan labarin, Hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, mai suna Frank Shuaibu, ya zargi gwamnonin APC da cewa barazanar da su ke yi cewa za su kulle bankunan da su ka ƙi karɓar tsoffin kuɗaɗe, hakan ne ya kai ga ƙara wa masu zanga-zanga ƙarin guiwar banka wa wasu bankuna wuta.
Ya ce wasu gwamnonin APC da su ka yi wannan barazanar ne su ka tunzira matasa yin tarzomar banka wa bankuna wuta a wasu garuruwan ƙasar nan.
Aƙalla gwamnonin APC 10 ne su ka maka Gwamnantin Tarayya ƙara kotu, inda su ka ƙalubalanci dakatar da karɓar tsoffin kuɗaɗe da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi tun a ranar 10 Ga Fabrairu.
Jihohin sun haɗa da Kaduna, Kogi, Zamfara, Legas, Katsina, Cross River, Ogun, Ekiti, Ondo da Sokoto.
Gwamnan Kaduna, Ogun sun yi fatali da CBN, su ka umarci a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe a faɗin jihohin su.
Sun kuma umarci bankuna su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗen ko kuma a ƙwace lasisin su a jihohin biyu.
Cikin jawabin da Shaibu ya fitar a ranar Litinin, ya ce Atiku ya ce wasu gwamnonin APC su na yi wa bankuna barazana, wanda hakan ne ya haifar da masu zanga-zanga fara farfasa bankuna da kuma banka masu wuta.