Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Bola Tinubu a APC, Kashim Shettima, ya koma gida ba tare da ya yi zaɓe ba, saboda rashin isar jami’an zaɓe da wuri.
Shettima wanda ya je bisa rakiyar Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, sun shafe minti goma a Rumfar Zaɓe ta 001 da ke Mazaɓar Lawan Bukar a cikin Maiduguri, ba tare da isar jami’an zaɓe ba.
Shettima ya koma gida ƙarfe 10 daidai na safiya.
Wannan jarida ta ruwaito cewa Peter Obi ya jefa ƙuri’a a Agulu, Jihar Anambra.
Ɗan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi, ya jefa ƙuri’a a garin su mai suna Agulu, cikin Jihar Anambra.
Obi wanda ya wa Atiku mataimakin ɗan takara a zaɓen 2019, ya na da magoya baya sosai a yankin sa.
Sai dai kuma ana hassshen tsagerun IPOB da ke haddasa fitina za su iya tayar da fitinar da za ta sa jama’a da dama su ƙaurace wa zaɓe a wuraren da ake gudun ɓarkewar tashe-tashen hankula.
Shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Bola Tinubu ya jefa ƙuri’a, har a wurin ya ce, “Ina da tabbacin ni zan yi nasara”, inji Tinubu bayan ya jefa ƙuri’a.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa ya na da yaƙinin shi zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Tinubu ya yi wannan kalamai a ranar Asabar, bayan ya jefa ƙuri’a Mazaɓar Bourdillion da ke Ikoyi, Legas.
Ya jefa ƙuri’a tare da uwargidan sa Remi Tinubu. Ya shaida wa manema labarai cewa, “Dimokraɗiyya ta zo da ƙafafun ta.”
Ya ce ya gamsu da yadda aikin gudanar da zaɓe ke tafiya ba bi wata tangarɗa.
Ya ce ya na da yaƙinin cewa shi ne zai yi nasara a wannan zaɓen.
A wani labarin, Buhari, Atiku, Remi Tinubu sun jefa ƙuri’un su.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ya jefa kuri’ar sa a Rumfar Zaɓe ta Ajiya 02, da ke Mazaɓar Gwadabawa, cikin Ƙaramar Hukumar Yola ta Arewa.
Ya bayyana wa manema labarai cewa ya na kyakkyawan zaton za a yi zaɓe lafiya.
Kuma ya nuna gamsuwa dangane da yadda ake gudanar da zaɓen ba tare da hatsaniya ko wata shan wahala ba.
A Daura, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jefa ƙuri’ar sa, inda ya haifar da dirama, yayin da ya ɗaga ƙuri’ar sa sama, da nufin kowa ya ga wanda ya dangwala wa ta sa ƙuri’ar.
A Legas, uwargidan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Remi Tinubu, ta jefa ƙuri’a, inda bayan zaɓe ta shaida wa manema labarai cewa Allah kaɗai ya san wanda zai yi nasara a zaɓen 2023 na shugaban ƙasa.