Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), ta bayyana cewa ba gaskiya ba ce labaran da ake watsawa cewa za ta kulle hanyoyin aikawa da kuɗaɗe ta wayoyin hannu da POS a lokutan zaɓe.
An dai yi ta yin wannan raɗe-raɗin cewa tun daga ranar 23 Ga Fabrairu za a kulle hanyoyin.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na NCC Reuben Muoka ne ya fitar da wannan sanarwar, inda ya ce jama’a su ci gaba da hada-hadar su, wancan labarin ƙarya ce, damfara ce kawai.
“Mu na bai wa jama’a masu harkokin kuɗi ta waya ko POS ko bankuna su ci gaba da harkokin su. Su yi watsi da duk wani sauƙin da ba daga NCC ya fito ba.”
“NCC ta samu tabbaci daga kamfanonin sadarwa cewa dukkan netiwak ɗin su zai ci gaba da aiki babu ƙaƙƙautawa, kuma ba ma za a samu wani cikas ba.”
Lokacin da aka riƙa yaɗa ji-ta-ji-tar, jama’a sun firgita tare da maida hankali wajen neman kuɗaɗen da za su yi cefanen da zai kai su har bayan gama zaɓe.
Sai dai kuma ganin har zuwa yammacin Juma’a, ranar jajibirin zaɓe ba a daina hada-hadar tura kuɗaɗen ba, yanzu hankalin jama’a ya kwanta.