Aƙalla ƙungiyoyin sa-ido kan zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya har 229 su ka tura wakilan su daban-daban domin lura da yadda zaɓen zai kasance.
A cikin ƙungiyoyin dai guda 196 duk na cikin gida Najeriya ne, saura guda 33 kuma daga ƙasashe daban-daban.
Jimlar yawan ‘yan sa-idon sun kai mutum 146,913.
Za A Yi Kankankan Ne Ko Wani Zai Yi Fintinkau?:
Zaɓen da za INEC za ta gudanar yau Asabar, 25 Ga Fabrairu, a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne zaɓen shugaban ƙasa na bakwai, bayan karɓar mulki daga hannun sojoji cikin 1999. An yi na farko a 1999, sai 2003, 2007, 2011, 2015 da kuma na 2019.
Mutum miliyan 93.2 ne ke da rajistar zaɓe, amma dai mutum miliyan 80 da wani abu ne su ka karɓi rajista. Daga cikin su ne kuma za su zaɓi wanda zai zama shugaban ƙasa a yau Asabar.
Tilas wanda zai zama shugaban ƙasa ya kasance ya fi saura yawan ƙuri’u, sannan kuma ya kasance ya samu aƙalla kashi 1 bisa 4 na ƙuri’un da aka kaɗa a aƙalla jihohi 24 daga cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.
Akwai jam’iyyu 18 masu takarar shugaban ƙasa. Amma dai ‘yan takarar APC, Bola Tinubu, PDP, Ariku Abubakar, NNPP Rabi’u Kwankwaso da LP, Peter Obi ne ake ganin za a fitar da shugaban ƙasa a cikin su. Saboda sun fi sauran ƙarfin yawan magoya baya nesa ba kusa ba.
Za a yi zaɓe a rumfar zaɓe 176,846, daidai da mazaɓu 8,809 a faɗin ƙasar nan.
Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Daura domin ya yi zaɓen sa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa, sauran ƙasashen takara duk sun tafi garuruwan su domin yin zaɓe a can.
Jami’an Tsaro:
Akwai jami’an tsaro da su ka haɗa jimillar kusan miliyan ɗaya, ciki har da sojoji masu sa ido domin tabbatar da zaɓe ta wanzu cikin kwanciyar hankali. A cikin su akwai ‘Yan Sanda 310,973, NSCDC 102,000, FRSC 21,783, Jami’an Kurkuku 11,336, NDLEA 9447, EFCC 380 da Jami’an ‘Imagireshin’ 21,600.
Matasan NYSC:
Daga cikin mataikata kusan miliyan ɗaya da rabi da za su yi wa INEC aiki, akwai matasan NYSC 200.
Zaɓen Sanatoci Da Wakilan Tarayya:
Akwai ‘yan takara sama da 4000 waɗanda su ma a yau Asabar za su fafata zaɓen sanata da na ɗan majalisar wakilan tarayya.
Za a zaɓi sanatoci 108 a yau Asabar, amma an ɗage zaɓen Sanatan Enugu ta Gabas sai ranar 11 Ga Maris.
Za a zaɓi ‘yan majalisar wakilai ta ƙasa 360 daga cikin ‘yan takara 3057.