Nayi wannan rubutun nawa ne ba don komai ba sai don na jawo hankalin al’umma duba da yadda na ga an buɗe yaƙin neman kuri’a na zaɓen 2023 da muke tunkara.
Nan ba da daɗewa ba al’umma za su fito da katin zaɓen su domin zaɓen ‘yan takarkarun da za su jagorance su a kujeru daban-daban a Najeriya.
Wannan ne ya sa nake ƙara jawo hankalin masu kaɗa kuri’a da kada su bari a saye yancin su.
Duk wanda ya karɓi kuɗi domin jefawa wani ɗan takara ƙuri’a kuma ya san wannan ɗan takarar ba wai ya cancanta ba ne to, ya sani muddin ya yi haka tamkar ya sayar da ‘yancinsa ne ga wannan ɗan takara.
Ka sani ko da wata rana idan ya ci zaɓe ka zo masa da buƙatun ku na cigaba da ku ke so a muku a yankinku wanda a ƙarshe zai iya ce muku kudin sa ne ya kawo shi kujerar da yake kai, ba don Allah ku ka zabe shi ba. Wannan kaɗan daga cikin walaƙancin da shugabannin da suka bada kuɗi aka zaɓa ke yi kenan.
Daga karshe, ina son in ƙara jan hankulan masu kaɗa ƙuri’a da su dinga dogon nazari a duk lokacin da ‘yan takara suke neman ƙuri’un su, domin zaɓen wanda ya cancanta, kar su bari a riƙa ruɗarsu da kuɗi, don hakan sayar da ‘yanci ne.
Allah ya taimake mu kuma ya bamu shugabanni nagari. Ameen.