Aƙalla tabbatattun bayanai sun nuna an kashe mutum huɗu a arangamar magoya bayan NNPP da APC a Kano.
Lamarin ya faru ne a kan titin Zaria Road, yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP ke tafiyar rangadin zagayen cikin birnin Kano, a ranar 23 Ga Fabrairu.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Kano, Kiyawa ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama mutum 85, tare da kama muggan makamai.
Ya ce tun da farko sai da ‘yan sanda su ka shiga tsakani don kada jam’îyyun su gwabza, amma hakan bai yi nasara ba.
“A ranar 22 ga Fabrairu 2023, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu rahoton cewa jam’iyyun APC, NNPP da PDP za su gudanar da rangadi cikin birnin Kano duk a ranar Alhamis, 23 Ga Fabrairu.
“Jin haka sai Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya gayyace su, inda aka shawarce su da su janye, saboda hatsarin da ka iya faruwa a Kano idan su ka ce za su yi rangadi su uku a rana ɗaya duk a cikin Kano.”
Kiyawa ya ce ba su amince da shawarar da ‘yan sandan su ka ba su ba.
Ya ce an kama mutum 85 da kuma muggan makamai, sai dai bai yi bayanin ko an kashe wasu ko wani ba.