Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu a ƙarƙashin APC ta ƙaryata wani rahoton da ya bayyana cewa dakarun EFCC sun kutsa wani gidan ƙarƙashin ƙasa na Bola Tinubu a Legas, inda su ka gano wurin da ya ɓoye naira biliyan 400.
Labarin dai wata jaridar yanar gizo ce ta buga shi, inda a ciki ta ruwaito cewa dakarun EFCC bisa umarnin Shugaban Ƙasa ta dira gidan Tinubu ta binciko wurin da a ɓoye naira biliyan 400 a ƙarƙashin ƙasa.
Jaridar mai suna www.igbotimesmagazine.online, ba ta bayyana ranar da abin ya faru ko wata ko lokaci ba.
Tuni dai sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Rundunar Kamfen ɗin TInubu, Bayo Onanuga ya ƙaryata labarin, wanda ita ma Hukumar EFCC ta ƙaryata, ta ce jami’an ta ba su kai farmaki gidan Tinubu ba.
Shafin jaridar na Tiwita dai ya na da nasaba da jam’iyyyar LP ta Peter Obi. A labarin dai ta ƙara da cewa Buhari ya bayar da umarni a gano kuma a kamo manajan bankin da ya bai wa Tinubu kuɗin.
Tuni dai ɓangaren Tinubu ya ce ƙarya ce, kuma ya yi kira ga jama’a su nisance irin waɗannan gidajen jaridun bogi, masu buga ƙarairayi don kawai su biya wa wasu mummunar aniyar su da buƙatun su.