Jakadadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta bayyana cewa ƙasar ta babu wani bambanci tsakanin manufofin manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa su huɗu, wato Atiku, Kwankwaso, Tinubu da kuma Peter Obi.
Ta ce Birtaniya ba ta goyon bayan kowane ɗan takara daga cikin masu takarar shugaban ƙasa su 18.
Daga nan ta ce Birtaniya za ta yi aiki tare da kowane ɗan takara ne ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 25 Ga Fabrairu, 2023.
Laing ta yi wannan kalamin ne a lokacin da ta ke tattaunawa a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata.
Duk da cewa akwai ‘yan takara 18, amma dai an fi ganin ɗaya daga cikin huɗun su Atiku, Kwankwaso, Tinubu da Obi nezai lashe zaɓen.
Laing ta ce babu wani bambanci dangane da manufofin dukkan ‘yan takarar manya guda huɗu, sannan kuma mafi abin da ƙasar nan ke fama da shi a yanzu shi ne matsalar tsaro da barazanar tattalin arziki.
Sannan kuma ta ce abu mafi muhimmanci shi ne ya zama tilas jama’a su amince da sakamakon zaɓen da ya kasance sahihi kuma karɓaɓɓe.
Kuma ta yi barazanar ƙaƙaba takunkumi ga shugabannin siyasar da zasu yi wa zaman lafiya barazana a lokacin zaɓe.
Idan ba a manta ba, INEC ta yi wa tawagar ‘Commonwealth’ alƙawarin gudanar da zaɓe sahihi.
A labarin, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ya tabbatar wa Thabo Mbeki za a gudanar da sahihin zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaban INEC ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da duniya cewa za a gudanar da sahihin zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya da duniya cewa za ta gudanar da sahihin zaɓe kuma wanda zai kasance karɓaɓɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya ƙara jaddada haka, lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Wakilin Sa-ido na Kungiyar Ƙasashe Rainon Ingila (Commonwealth), ranar Litinin a ofishin sa da ke Hedikwatar hukumar a Abuja.
“Tuni INEC ta fahimci muhimmancin gudanar da sahihin zaɓe, ba ma a Najeriya kaɗai ba, har a nahiyar Afirka baki ɗaya.
“Gudanar da zaɓe a Najeriya babban aiki ne. Amma kamar yadda na ce, nauyin gudanar da wannan gagarimin aiki ya na a wuyan mu.
“Muhimmancin gudanar da sahihin zaɓe bai tsaya wajen samar da wanzuwar zaman lafiya da nagartacciyar gwamnati kaɗai ba. Tasirin sahihin zaɓe a Najeriya ya shafi har sauran ƙasashen Yammacin Afirka.
“Ina tabbatar maku da cewa ba za mu taɓa yarda mu bai wa Najeriya da duniya kunya ba.” Haka Yakubu ya shaida wa Shugaban Wakilan Sa-idon Kasashe Rainon Ingila, Thabo Mbeki, wanda tsohon Shugaban Ƙasar Afrika ta Kudu ne.
Yakubu ya kuma jinjina wa irin gudummawar da ƙungiyar ta ke bayarwa ta hanyar turo wakilan sa-ido masu lura da zaɓuɓɓukan da INEC ke gudanarwa a Nijeriya.
Ya ce Najeriya ta amfana sosai daga shawarwarin da ƙungiyar ke bayarwa a zaɓuɓɓukan da Najeriya ta gudanar a baya.
Da ya ke jawabi, Mbeki ya ce maƙasudin zuwan su Najeriya shi ne sa-ido da lura da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya gudana, sannan kuma a ƙarshe su bayar da rahoto a rubuce.
“Wannan shi ne zai kasance zaɓe na bakwai tun bayan samun ‘yanci a Najeriya. Zaɓen ya na da muhimmanci ga ita kan ta da kuma Afirka baki ɗaya.
“Dalili kenan mu ke zuwa domin ganin yadda zaɓe ke gudana, mu koma mu kai rahoto. Amma mu na da yaƙinin cewa za a gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana.”