Kotun Koli ta baiwa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan takarar kujerar sanata ta Yobe ta Arewa.
Da yake yanke hukuncin alƙalin kotun mai shari’a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun hujjojin a bayyane na zargin aikata maguɗi a zaɓen fidda da gwanin da aka yi ta wannan kujera.
Kotun Kolin ta ce hukuncin kotun Ɗaukaka kara bai dace a dalilin haka ta wancakalar da shi.
Alkalai biyu da suka barranta kansu daga hukuncin da kotun ta yanke cikin Alkalai biyar ɗin da suka yi zaman yanke hukuncin, sun ce ba su yarda cewa Ahmed Lawan ne ya yi nasara a zaɓen fidda gwanin.
Alkali, Jauro ya ce, Ai tun farko ma, Ahmed Lawan bai yi takarar kujerar ba, saboda haka bashi da hurumin dawowa ya ce kuma yana so bayan an gudanar da zaɓen fidda gwani wanda hukumar zaɓe ta halarta.
” Ahmed Lawan takarar shugaban kasa ya yayi, bai ma yi takarar kujerar sanatan Yobe ta Arewa ba, kwatsam ba zai zo kuma bayan ya ci kasa a can ba ya ce kuma shine ɗan takara a nan. Ni ban yarda ba, in ji daya daga ciki Alkalan da suka barranta kansu daga hukuncin da alkalan kotun kolin suka yanke.
Alkalai 3 cikin 5 da suka yanke hukuncin ne suka ce Ahmed Lawan ne sahihin ɗan dakarar Yobe ta Arewa, biyu kuma sun ce basu amince da hakan ba.
Idan ba a manta ba Jam’iyyar APC ce dai ta ƙalubalanci Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ɗan takara.
Discussion about this post