Rundunar ‘yan sandan babban birinin tarayya Abuja sun kama Uche Aigbe faston cocin ‘House on the Rock’ dake Abuja tare da wasu mutane biyu a cocin bisa laifin mallakar makami ba tare da lasisi ba.
Bisa ga wani takarda da rundunar ta fitar ranar Litini Jami’ar hulda da jama’a na rundunar Josephine Adeh ta bayyana cewa rundunar ta kama Agibe ranar Lahadin da ya gabata bayan karar da wani ya kawo a ofishin ƴan sandan.
Josephine ta ce mutane sun afka cikin ruɗani a lokacin da suka ga wannan fasto ya hau minbari dauke da bindiga kiran AK-47 a hannun sa a cocin.
Hotunan faston rike da bindigan ya kareda kafafen sada zumunta dake yanar gizo.
Josephine ta ce masu amfani da kafafen sada zumunta a yanar gizo sun ce wa’azin da Agibe ya yi a ranar Lahadin wa’azi ne da ka iya tada zaune tsaye a al’umma.
Ta ce daga cikin mutum biyu din da rundunar ta kama tare da faston akwai Malan Audu dansandan dake aikin samar da tsaro a cocin wanda a hannun sa ne faston ya karbi bindigar aro.
Malan Audu ya bai wa faston bindigarsa ba tare da ya sanar ko ya nemi izinin rundunar ‘yan sandan Abuja ba.
Discussion about this post