Kotu a Kado Grade I Area dake Abuja ta gurfanar da Abdulrazak Lawal bayan ‘yan sanda sun kama shi da laifin sace wayar wata karuwa a jabi.
‘Yan sandan sun kama Lawan bisa laifukan sata da damfarar karuwa.
Sakamakon binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna wayar karuwar da Lawal ya sace kirar iPhone ne da kudinsa ya kai Naira 266,000.
Dan sandan da ya shigar da karar Stanley Nwafoaku ya ce Charity Joseph dake zama a Jabi Masalachi ta kawo karan satar da Lawal ya yi a ofishin su dake life Camp ranar 30 ga Janairu da misalin karfe 3 na rana.
Nwafoaku ya ce Charity ta bayyana cewa a ranar 25 ga Janairu Lawal ya nemi Charity inda suka yi yarjejeniyar cewa zai biya ta Naira 10,000 indan ta kwana da shi a otel din White House dake Daki Biyu a Jabi.
Ya ce Charity ta ce ta farka da safe ne ba ta ga Lawal ba kuma bai biyata Naira 10,000 da suka yi cikin zai biya ta ba sannan ya waske da wayar ta iPhone.
Nwafoaku ya ce da ya shiga hannun jami’an tsaro Lawal ya amsa cewa shine ya dauke wayar Charity amma ya siyar wa wani Abba da ya gudu zuwa Katsina akan Naira 35,000.
Sai dai kuma daga baya a Kotu Lawal ya musanta laifukan da ake zargin sa da su.
Alkalin kotun Muhammed Wakili ya bada belin Lawal kan Naira 150,000.
Za a ci gaba da shari’a ranar daya ga Maris.
Discussion about this post