‘Yan bindiga sun Kai wa wasu ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe zaɓe hari a makarantar firamare dake Tudunwada a jihar Gombe ranar Juma’a.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Mahid Abubakar ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES.
Maharan sun ji wa mutum uku daga cikin ma’aikatan rauni sannan har an kai su asibiti likitoci na duba su.
Wani ma’aikacin INEC ɗin da baya so ya fadi sunnan sa ya ce maharan sun kwace wayoyin salula guda uku, jakunan baya da na’uran cajin wayar wato ‘power Bank’ guda uku daga hannun su.
Ya ce ma’aikatan hukumar da dama sun ji rauni a jikinsu yayin da suke arcewa a lokacin da maharan suka kawo musu hari.
“A Lokacin da maharan suka afka mana mun nemi jami’an tsaro a fadin makarantar firamaren mun rasa.
Ya ce maharan sun kawo musu hari da misalin karfe 11 na dare amma jami’an tsaro ba su kawo musu dauki ba sai bayan da maharan suka tafi.
Babu tabbacin ko wannan harin zai shafi yadda mutane za su fito domin kada kuri’ar su a zaben Shugaban kasa da za a Yi ranar Asabar.
Duk da haka hukumar INEC ta tabbatar wa mutane cewa a shirye take domin lamari cikin gaggawa.
A ranar Asabar ne Najeriya za ta zabi Sabon Shugaban kasa Wanda zai jagoranci mulkin kasan na tsawon shekarun hudu masu zuwa.