Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe ‘yan banga da aka fi sani da ‘Yansakai’ a dajin Yargoje.
Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka a wata takarda da ya saka wa hannu a garin Katsina.
“A ranar 1 ga Fabrairu ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 suka kai wa gidan Alhaji Muntari dake Unguwar Audu Gare a Kandarawa dake karamar hukumar Bakori da a nan suka saci shannu 50 da tumaki 30.
“A ranar 2 ga Faburairu ‘yan kungiyar sun fantsama yin farautan maharan domin kwato dabbobin da maharan suka sace.
“Jami’an tsaro sun bi sawun maharan har zuwa dajin Yargoje inda maharan suka fito suka yi wa ‘yansakan zobe suka kashe su duka.
“maharan sun kashe ‘yan sakai 41 sannan wasu mutum biyu sun ji rauni.
“Kwamandan Malumfashi da ‘yan sandan suka kwashe gawarwakin ‘yansakan da suka mutu sannan mutum biyu din da suka ji rauni na babban asibitin Kankara.
Isah ya ce hadaddiyar kungiyar jami’an tsaro sun fara farautar maharan domin kamo su da hukunta su.