Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala bincike kan Khadija Rano wacce ake zargi da kashe aurenta don ta aure saurayin diyarta
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Lawan Ibrahim ya sanar da haka ranar Talata a garin Kano cewa kwamitin da aka naɗa ya kammala binciken sa ya kuma mika rahoton sa.
Ibrahim ya ce Shugaban kwamitin da aka nada domin gudanar da bincike kan Khadija kuma mataimakin Shugaban hukumar Malam Hussain Ahmed ya ce kwamitin ya gano cewa auren ya halasta kuma ya cika dukkan ka’idojin da ake bukata.
Ahmed ya ce bayan mijin Khadija ya sake ta Kuma ta kammala iddah na watanni uku kamar yadda Musulunci ya tanada ne ta auri saurayin diyarta wanda sun rabu da ƴarta.
Ya Kuma karyata zargin da mutane ke yi wai Khadija ta fara nuna soyayya ga shi saurayin ɗiyar ta ta tin bata fita daga gidan tsohon mijin ta ba.
“Auren ya halasta a addinin Musulunci da hakan ya sa kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano da kansa ya ce abinda ya faru a tsakanin ma’auratan na aure ya yi daidai a musulunci.
Shugaban hukumar Harun Ibn-Sina ya yaba wa kwamitin kan yadda suka dauke nauyin da ya rataya a kan su.
Malam Ibn-Sina ya ce an zabo ‘yan kwamitin a tsanake saboda zurfin ilimin da suke da shi na koyarwar addinin Musulunci da fahimtar al’umma.
Ya ce ya kamata jama’a su daina yada labaran karya su kuma nisanta kan su da rashin fahimtar al’amuran da suka shafi Musulunci.