Ɗan takarar shugabancin Najeriya a APC ya yi nasarar lashe ƙuri’u 421,390 a Jihar Jigawa.
Atiku Abubakar na PDP ya samu 386,589. Hakan ya nuna bambancin tazarar ƙuri’u 34,803 a tsakanin su.
Jam’iyyar NNPP ta samu 98,234, yayin da Peter Obi na LP ya samu 1,889.
A jihar Kano kuwa tun ba a kammala ƙidaya ba NNPP ta ba PDP tazarar ƙuri’u 650,000, Peter Obi 8,926 kacal.
Can a Jihar Adamawa kuwa, Atiku ya lashe ƙananan hukimomi 11, Peter Obi 1, ana jiran sakamakon sauran 10.
Bayan kammala tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 12 na Jihar Adamawa daga cikin 20 ɗin da jihar ke da su, Atiku Abubakar na PDP kuma ɗan asalin jihar ya lashe ƙananan hukumomi 11.
Peter Obi na LP ya lashe sakamakon Ƙaramar Hukumar Numan.
PDP ta lashe Lamurde, Gerei, Shelleng, Guyuk, Toungo, Ganye, Mayo-Belwa, Song, Demsa, Fufore da Yola ta Kudu.
Atiku ya samu ƙuri’u 213,117, APC kuma 99,898, sai LP 56,857. NNPP ta tashi da 3,609.