Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta iƙirarin da aka danganta da shi, inda aka ce ya ce a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe na naira 500 da naira 1000.
CIkin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran CBN, Osita Newnisobi ya fitar a ranar Juma’a, CBN ya ce maganar ta bogi ce, kuma ƙarya aka yi wa bankin.
A ranar Juma’a ɗin ce dai wasu rahotanni su ka ruwaito CBN ya ce bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar naira 500 da naira 1000 tsoffi.
Haka ma har rahoton ya ce CBN ya ce aƙalla amma sai daga naira 500,000 za a karɓa a hannun mutum, kuma sau ɗaya tilo.
Sai dai kuma a martanin da bankin ya bayar a ranar Juma’a, CBN ya ce rahoton ƙarya ce kawai, ba ta umarci bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗen ba.
“Mu dai mu na nan a matsayin mu kan jawabin da Shugaban Ƙasa ya yi a ranar 16 Ga Fabrairu, 2023, don haka naira 200 kawai aka bai wa CBN umarnin ci gaba da amfani da ita a ƙasar nan har zuwa kwanaki 60 nan gaba, wato 10 ga Afrilu, 2023.
“Mu na kira ga jama’a su yi watsi da batun ci gaba da kai tsoffin naira 500 da naira 1000 banki, kai da ma duk wata sanarwa kan tsoffi da sabbin kuɗi in dai ba daga CBN aka yi sanarwar kai-tsaye ba.”
Daga nan CBN ya umarci kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatarwa su na tantance labarai kafin su buga.
Bincike ya tabbatar cewa ‘yan Najeriya masu ɗimbin yawa na ajiye da tsoffin kuɗaɗe saboda matsalar ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
Tuni dai Kotun Ƙoli ta hana CBN ƙin tsoffin kuɗaɗe, amma kuma bankin ya yi kunnen-uwar-shegu da umarnin kotu.
Kasuwanci da harkokin yau da kullum manya da ƙanana duk nema su ke su tsaya cak, yayin da wasu da dama su ka taƙaita yin zirga-zirga maras dalili.
A ranar Alhamis Shugaba Buhari ya bada umarnin a ci gaba da karɓar tsoffin naira 200. Ranar Juma’a kuma aka riƙa watsa sanarwa a soshiyal midiya cewa bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar naira 500 da naira 1000. Amma daga baya sai CBN ya fito ya ƙaryata.
Discussion about this post