Ɗan Takarar Shugabancin Ƙasa a inuwar Jam’iyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce tushensa a matsayin ɗa ga ƴar kasuwa ne ya bashi damar fahimtar matsalar da canjin kudi ya kawowa a tsakanin al’umma.
A takarda da ta fito daga ofishin watsa labarai na ɗan takarar wanda AbdulAziz AbdulAziz ya saka wa hannu ranar Asabar, ya ce, Tinubu, wanda a lokaci mabanbanta ya bayyana rashin dacewar sabon tsarin, ya ce a matsayinsa na wanda ya tashi a kasuwa, ya fahimci yadda yanayin zai yi ta’asiri a rayuwar masu ƙaramin ƙarfi.
Da yake bayani a yammacin ranar Juma’a yayin wani taron ganawa da shugabannin yan kasuwa na ƙasa a Babban Birnin Tarayya Abuja, Ɗan Takarar na Jam’iyar APC ya ce mahaifiyar sa ta ciyar da shi da ilimantar da shi da kuɗin kasuwanci, ya kara da cewa yana iya fahimtar faduwa da riba na yan kasuwa.
Tinubu ya ce yana da masaniyar rashin zagawar wadatattun kuɗaɗe zai iya kawo tasgaro a tattalin arziki na yau da kullum.
Ya bayyana tausayawarsa ga ƙananun ƴan kasuwa tare da ƴan kasuwa da ke mu’amula da abubuwa masu saurin lalacewa, in da ya ce sune waɗanda tsarin zai fi shafa.
Tinubu ya bada misali da wani mai sayar da karas da ya hanga a yayin yawon neman zaɓe da ya tafi a Jihar Gombe, wanda ke tsaye kan kayansa a cikin rana ba tare kowa mai neman sayen kayan ba, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda rashin kuɗi a hannun jama’a.
Ɗan takarar shugabancin ƙasar yayi kira ga ƴan kasuwa da kada su bari matsalar canjin kudin ya tunzura su.
Ya ce Idan har yayi nasarar lashe zaɓensa to zai kirkiri hanyar bayar da bashi mai sauƙi ga ƴan kasuwa tare da share musu dukkannin wata matsalar da ta addabe su a kasuwancinsu.
Tinubu ya baiwa ƴan kasuwar tabbaci cewa ya san inda ke yi musu ƙaiƙayi kuma zai magance musu a matsayin sa na wanda ya fito daga gidan kasuwanci.
Wakilan shugabannin ƴan kasuwan da suka yi jawabi ga mahalarta taron sun bada kyakkyawar shaida a kan ɗan takarar wanda suka kira a matsayin daya daga cikin su.
Sun yi alkawarin bayar da ƙuri’u masu yawa domin nasarar Tinubu, wanda suka bayyana a matsayin wanda yafi sauran ƴan takarar nagarta.
Tinubu ya halarci Taron tare da Gwamnonin da suka hada da Muhammad Badaru Abubakar (na Jigawa) da Abubakar Sani Bello (na Neja), tare da sakataren majalisar yakin neman zabensa Hon. James Faleke, da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iya.