Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya na so ‘yan Najeriya su zaɓi ɗan takarar APC, Bola Tinubu, saboda ya naƙalci ƙasar nan cikin ta da bayan ta.
Haka Buhari ya bayyana a lokacin da ya ke jawabi a Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, a ranar Alhamis, a Sokoto.
Buhari ya ce Tinubu ya kyautata wa ɗimbin mutane masu yawa, kuma ba shi yin la’akari da addinin mutum ko bambancin addini.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Abdul’aziz Abdul’aziz ya sa wa hannu, ya ƙara da cewa Buhari ya ce Tinubu makusancin sa kuma aminin sa ne na lokaci mai tsawo, kuma ya nuna ya na da gogewar da zai iya riƙe shugabancin Najeriya.
“Tinubu ya naƙalci Najeriya sosai, a ko da yaushe ya na taimaka wa jama’a, ko ma daga ina mutum ya fito, ba tare da yin la’akari da bambancin ƙabilanci ko addini ba.” Haka Buhari ya shaida wa Sarkin Musulmi a Sokoto.
“Na karaɗe jihohin Nasarawa da Katsina tare da Tinubu, kuma ga ni yau nan Sokoto tare da shi. Kuma daga nan za mu rankaya duk inda ya kama. Shi ne ɗan takarar jam’iyyar mu. Saboda haka tilas mu goya masa baya kenan.
Buhari ya ce ‘Asiwaju ya naƙalci Najeriya ciki da bayan ta’.

“Mun zo ne domin neman wa Tinubu goyon baya. Kuma na tabbata za mu samu wannan taimako da mu ke nema,” inji Buhari.

A nasa jawabin, Tinubu ya yi alƙawarin kawar da ‘yan bindiga kuma ya yi alƙawarin bunƙasa harkokin noma.