Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu ya yi wa Katsinawa alƙawarin kakkaɓe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, idan ya yi nasarar lashe zaɓe a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Tinubu ya yi wannan alƙawari a ranar Litinin, lokacin da ya ke kamfen a Katsina. Wurin kamfen ɗin dai ya koma wurin addu’o’in neman sauƙin ‘yan bindiga, saboda a makon ne aka kashe sama da ɗan sakai 100 a Ƙaramar Hukumar Bakori, Jihar Katsina.
Sai dai su kuwa ‘yan sanda sun bayyana cewa mutum 42 kaɗai aka kashe.
Tinubu ya ce an ci gaba da kamfen ɗin ne a bisa shawarar Gwamna Aminu Masari, domin shi ne ya ce idan aka tsayar da kamfen saboda kisan da ‘yan bindiga su ka yi, to tamkar an miƙa wuya ne sun yi galaba kenan.
Tinubu ya jinjina wa waɗanda su ka halarci kamfen ɗin, duk kuwa da halin ƙuncin rayuwar da ake ciki a ƙasar nan.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Abdul’aziz Abdul’aziz ya fitar, Asiwaju ya ce a zaɓi APC, kada a bari PDP jam’iyyar da ta ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya yunwa ta sake kafa gwamnati.
Shi kuwa Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan sakai 42 da ‘yan bindiga su ka kashe a Katsina, sun zama shahidai’.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah–wadai da ‘yan bindigar da su ka kashe ‘yan sakai 42 a Jihar Katsina.
Ita ma Gwamnatin Jihar Katsina ta ce za ta kafa kwamitin da zai binciki musabbabin kisan ‘yan sakai ɗin.
Cikin wata sanarwa da Garba Shehu, Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari ya fitar a ranar Lahadi, ya ce Buhari ya yi matuƙar jimamin kisan mutanen 42, kuma ya miƙa ta’aziyya ga iyalan su.
Buhari ya ce waɗanda ‘yan bindigar su ka kashe, mun yi mutuwar shahada, tunda an kashe su a ƙoƙarin kare maɓarnata afkawa ƙauyen su.
“Mu na jimami da addu’a da kuma ta’aziyya ga iyalan ‘yan sai waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe. Allah ya gafarta masu.” Inji Buhari.
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana sanarwar kafa kwamitin gano musabbabin kisan ‘yan sakai ɗin su 42.
Mashawarcin Harkokin Tsaro na Gwamnan Katsina, Ibrahim Katsina ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Asabar da dare, yayin da ya ke magana kan wannan kisan gillar.
Ibrahim, wanda tsohon jami’in SSS ne, ya ce an kashe ‘yan bindiga da dama a mummunan gumurzu.
Ya ce maƙasudin kafa kwamitin shi ne domin ya gano abin da ya kai ga yin wannan mummunan kisan gilla.
Yadda Aka Yi Kisan Gillar ‘Yan Sakai 42 A Katsina:
Rundunar ‘Yan Sandan ta fitar da sanarwar yadda aka yi kisan gillar.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Katsina, Gambo Isa, ya ce ‘yan an kai hari ne ranar Laraba da dare a ƙauyen Kandarawa, inda su ka dira gidan wani tattajirin kauye, kuma ɗan kasuwa, cikin Ƙaramar Hukumar Bakori, su ka kwashi shanu 80.
“Sun kai hari ne gidan Alhaji Muntari a Unguwar Audu Gare, cikin garin Kandarawa. Sun buɗe wuta tare da kama shanu 50 tumaki 30.”
Gambo Isa ya ce wannan hari da aka kai ya harzuƙa ‘yan sakai, waɗanda su ka yi shiri su ka bi ‘yan bindigar su ka fara musayar wuta, a ƙoƙarin su na ƙwato dukiyar da aka sata.
“A ranar 2 Ga Fabrairu kuma sai wajen ƙarfe 10 na dare ‘yan sakai daga ƙauyuka 11 su ka yi gangami su ka nausa farautar ‘yan bindigar.
“Sun bi sawun ‘yan bindigar har Dajin ‘Yargoje. Sai dai abin takaici ba su sani ba ashe ‘yan bindigar sun yi masu kwanton-ɓauna, su ka bindige mutum 41, biyu kuma su ka ji raunuka.”
Discussion about this post