Ƙaramin Ministan Ƙwadago, kuma Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Kamfen ɗin TInubu, Festus Keyamo, ya maida wa tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara cewa, ya girme masa a aikin lauya.
Ya ce, “don haka ka kaina auna girman mutum da yawan shekarun da ya shiga siyasa, ko yawan zaɓen da ya taɓa lashewa ko ya yi takara ya faɗi.
Keyamo ya yi wa Dogara wannan raddi a shafin sa na Tiwita.
“Bari na tuna maka, na kai ƙololuwar mataki a aikin lauya, saboda haka tilas ka koyi yadda za ka riƙa girmama na gaba da kai a fannin shari’a da aikin lauya.” Haka Keyamo wanda babban lauya ne (SAN), ya rafka wa Dogara wannan raddin.
Dogara da Keyamo dai duk ajin su ɗaya a Makarantar Koyon Aikin Shari’a da Lauya ta Najeriya.
“E, tabbas ni da kai ajin mu ɗaya a Makarantar Lauya. Amma ina jiran sai ranar da ka fara fitowa takara ka ci ko da kujerar kansila ce tukunna, sannan za ka fara kiran kan ka tsara ta a siyasa. Kuma ka san wadan da za ka riƙa yin kokawa da shi, ba iri na ba. Ni na fi ƙarfin ka.” Haka Dogara ya kamtsa wa Keyamo wannan gora bisa kai, wadda wannan dukan ne ya fusata shi maida wa Dogara raddi.
Dogara ya rafka wa Keyamo gora ce bayan Minista Keyamo ɗin ya kira shi karuwan ɗan siyasa, mai yawon gallafiri da cin amana, saboda ya na ragargazar APC da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu.
Shi kuma Keyamo ya ce Dogara ya maida nasarorin da Keyamo ya samu a fannin lauya aikin banza, abin da Keyamo ɗin ya ce cin zarafin miliyoyin ‘yan Najeriya ne.
Discussion about this post